Al'amarin rashin tsaro a Najeriya ya dauki wata fuskar ban tsoro ta yadda sama da kananan hukumomi 40 a sassa daban-daban na kasar ke karkasin ikon 'yan bindiga, 'yan ta'adda da 'yan bindiga ne da ba a sani ba.
Wuraren dake karkashin ikon 'yan ta'addan suna cikin jihohin Kaduna, Zamfara, Niger, Katsina, Sokoto, Abia da Imo.
Wannan lamari babu shakka babbar barazana ce ga zaben 2023 ballantana tsaron ma'aikatan zabe da masu kada kuri'u a inda 'yan ta'adda ke mulka ba abu bane mai tabbas.
A jihar Kaduna, wasu kauyukan jihar duk jama'a sun bar su sakamakon lamurran ta'addanci a jihar, Punch ta rahoto hakan. Kananan hukumomi kamar Chikun, Kajuru, Kachia, Zangon Kataf, Kauru, Lere, Birnin Gwari da Giwa duk suna fuskantar farmakin 'yan ta'adda.
Kananan hukumomin Zamfara da ta'addancin 'yan bindiga 'yan ta'adda yayi kamari kuma za a iya cewa suna cin karensu babu babbaka a dukkan kananan hukumomin jihar.
Daga cikin kananan hukumomin da lamarin yafi kamari akwai: Maru, Tsafe, Bakura, Anka, Maradun, Gusau, Bukkuyum, Shinkafi da Bungudu.
A yayin zantawa da jaridar Punch, wani mazaunin kauyen Babbar Doka dake karamar hukumar Maru, Malam Ibrahim Abubakar, yace zai yi wuya su iya fita zaben 2023.
A jihar Niger, kananan hukumomi bakwai ne ke fama da hare-haren 'yan ta'addan. Sun hada da Rafi, Munyan, Shiroro, Magama, Mashegu, Mariaga da Wushishi yayin da 'yan Boko Haram suka kafa tuta a Shiroro.
Wasu daga cikin jama'ar yankunan sun ce sun gigice sakamakon rashin tsaro wanda yasa suka tsere tare da barin gidajensu. Kananan hukumomin Katsina Bincike ya nuna cewa, 'yan ta'adda sun kara yawan wuraren suke kai hari bayan kananan hukumomi takwas da suke cin karensu babu babbaka a Katsina.
Kananan hukumomin su ne: Batsari, Jibia, Danmusa, Safana, Kankara, Dandume da Faskari inda suka zarta har Dutsinma, Kurfi, Batagarawa, Rimi, Danja, Kafur, Matazu, Kaita, Malumfashi da Katsina.
Sokoto a kalla kananan hukumomi 11 daga cikin 23 na jihar Sokoto suna fama da rashin tsaro.
Kananan hukumomin da lamarin ya shafa sun hada da Illela, Rabah, Sabon-birni, Isa, Wurno, Gada da Goronyo.
Sauran sun hada da Tangaza, Gudu, Denge-shuni da Kebbe yayin da Shagari da Yabo farmakin bai tsananta ba.