Ba Zan Taba Yafewa Wanda Ya Yi Sanadin Rasa Kafa Ta Ba---Fatima Suleiman

Ba Zan Taba Yafewa Wanda Ya Yi Sanadin Rasa Kafa Ta Ba---Fatima Suleiman

A ranar Alhamis data gabata wani matashi Aliyu Sanusi Umar ya take kafar matashiya Fatima Suleiman a lokacin da yake wasa da mota abin da yay i sanadiyar mayar da ita gurguwa in da aka yanke kafarta ta dama.

Lamarin ya jefa mutane cikin alhini da jimamin abin da ya faru ga matashiyar da shekarunta bas u fi 20 ba a ranar da ta kammala sikandare.

Aminiya ta ziyarci matashiyar asaman gadon asibitin koyarwa ta Usman Danfodiyo in da take jinya domin sanin yanda lamarin ya faru ta ce “a ranar Alhamis bayan kammala jarawabarmu ta NECO  a Khalipha International School wadda take ta karshe ne, sai muka fito waje domin a cikin makarantar ana wasa da ruwa, murnar kare makaranta, bayan na kira mamata ta zo ta dauke ni, muna a zaune a gefen makaranta ni da kawayena biyu  anan ne yaron suka zo shi da abokansa ba dan makarantar ba ne amma  yana tare da ‘yan makarantarmu  suna wasa da mota suna gudu a lokacin da ya tun karo ni ina zaune kafin na tashi ne  sai ya taka kafa ta ya wuce abinsa, hankalina bai gushe ba har aka kawo ni asibiti aka cire kafa ta.”

Ko kin yafe abin da wannan yaron ya yi maki? Ta ce “Gaskiya ba zan iya yafe masa ba saboda ya riga ya halakamin rayuwa, bani da kafa daya, ina neman taimako a gyara min kafa ta, don cigaba da rayuwa.

“Ina son gwamnatin Sakkwato ta taimakawa lafiya ta a kuma hukunta wanda ya yi min haka,” a cewarta.

Wannan abin da ya same ki ko ya karya zuciyarki da son cigaba da karatu? Ta ce “In sha Allah zan cigaba har sai na cimma burina na zama cikakkiyar likita, don taimakawa al’umma ta. Ina son a taimaki rayuwata, yakamata uwaye su rika kula da yaransu a wannan zamani.”

Ya za ki kwatanta rayuwarki a yanzu da kafin faruwar haka? Ta zubar da hawaye ta ce “ina cikin damuwa gaskiya domin ban saba da irin wannan rayuwar ba, amma na yi tawakkali domin kaddarar Allah ce ba wanda ya isa ya hana faruwar haka, da ni da duk wanda zai samu kadara irin haka kawai a yi hakuri a dauki kaddara, abin da ya faru, ni nabarwa Allah komai,” a cewar Fatima.

Hukumar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta tabbatar za ta gabatar da matashin a gaban kotu, jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Sanusi Abubakar ya sanr da hakan ga manema labarai a ranar Assabar data gabata.

Ya ce rundunarsu ta samu labarin hatsarin ne ta hannun hukumar makarantar  da hanzari jami’ansu suka dauki matakin kama direban.

Ya ce sun kammala bincikensu za su gurfanar da matashin a gaban kotu domin yin adalci.