'Yan bindiga suna cin karensu ba babbaka a Gabascin Sakkwato musamman a karamar hukumar Sabon Birni in da suka kashe mutum 12 da tarwatsa kauyukka 14 a bangaren, kamar yadda manema labarai suka samu labari.
Sabon Birni tana bangaren Gabascin jihar Sakkwato mahara suna addabarsu tsawon shekarru abin da ya sanya da yawan magidantan dake yankin komawa kasar Nijar domin samun nutsuwa.
Tsohon shugaban karamar hukumar Sabon birni Idris Gobir ya ce fiye da mutum 10 aka kashe a sati daya an sace dabbobi sama da 1000.
Ya ce kauyukkan da suka koma kufai a yankin sun hada da Garin Abara, Unguwar Abzin, Garin Namaimai, Garin Amadu, Garin Danjari, Gidan Buta, Kalage, Kaihin Aska, Rukkumi da Garin Dubu.
Sauran sun hada da Kyara da Naguliya, Garin Boka da Kyalkyale dukkansu ba za ka samu mutum ko daya acikinsu ba, mafiyawansu suna kasar Nijar wurin gudun hijira.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce an kashe mutum 12 a gefen cikin sati biyu.
Manema labarai sun samu labarin an harbe mutum biyar daya ya rasu sauran suka samu raunukka suna karba magani a asibiti.
A 7 Juli maharan sun kashe mutum uku Alhaji Aware, Zayyanu Dalha da Malama Ladi.
'Yan bindigar sun kai hari a garin Dangari a gudunmur Gatawa a ranar Jumu'a 30 ga Juli sun kashe mutum uku Alhaji Amadu da Sanusi Dan biba da Malam Janyo, sun kashe wasu mutum uku a kauyen Kalage a 4 ga watan Agusta sun hada da Bilya Agada, Isaka Suntau da Rufa'i Ibrahim. A kauyen Zurudu Shamsu Halilu.
Sun kashe mutum daya a garin Idi Ayuba Muhammad sun ka tafi da babur dinsa, suka raunata Abdussalamu Ummaru an kwantar da shi a asibitin Maradi ta jihar Nijar.
A lahadin da ta gabata maharan sun kashe mutum uku a kauyen Tarah da Garin Hullo, suna cikin kauyukkan daga karfe 8 zuwa 10:30 na dare.
A bayanin da aka samu Maharan sun cilastawa mutanen Makuwana su biya fansar miliyan biyu kar akai musu farmaki, amma sun yi kashe kashe da garkuwa da mutane a yankin.
Kwamishinan harkokin tsaro a Sakkawato Kanal Garba Moyi ya tabbatar da hare-haren ya ce Maharan sun kai farmaki a Tangaza da Illela da wasu bangarorin jiha.
Da Rana Tsaka Karfe 2:45 na ranar yau Talata 'yan bindiga Dauke da Munanan bindigogi sun afka cikin garin Ta Girke dake Gundumar Unguwar Mai Lalle dake Karamar Hukumar Sabon-birni Sun Budewa ƙauyen Wuta.
Rahoto ya bayyana cewar sun harbi mutun biyu Kuma sun fatattaki mutane dake cin Kasuwar garin a yau Talata haka ma sun karbe baburan mutane.