Mu Baiwa Gwamnatin Tambuwal Wa'adin Sati Biyu Ta Kwashe Sharar Da Ke Kan Titin Maituta---Bajare

"Idan wa'adinmu ya cika ba a kwashe ba, za mu nemi da gwamnati ta gaya mana wurin da za mu zuba sharar bayan mun kwashe ta, don kaucewa laifi, mu zuba a bayan gari ta ce ba a can ne take so ba, ko mu rika kaiwa manoma a gonakinsu ta ce ba haka ta so ba, kan wannan aikin muna son a bi ka'idar gwamnati don ba fada muke da ita ba, muna son bayar da tamu gudunmuwa ne ga abin da muke ganin an kasa", a cewar Bajare. Ya ce ba daidai ba ne a zuba ido ana kallon mutane suna cutuwa kan abin da in an hada kai ana iya kawar da shi, sharar nan ta addabi mutanen unguwar nan matuka ta kawo masu ci baya a haujin tattalin arzikinsu da lafiyarsu

Mu Baiwa Gwamnatin Tambuwal Wa'adin Sati Biyu Ta Kwashe Sharar Da Ke Kan Titin Maituta---Bajare
Sharar Maituta

Tsohon Dan majalisar dokokin jihar Sakkwato jigo a jam'iyar APC Honarabul Malami Muhammad Galadanchi wanda aka fi sani da Bajare ya baiwa gwamnatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal wa'adin sati biyu kan ta kwashe sharar da ke kan titin Maituta a cikin birnin jiha da ta addabi mutanen unguwar, ko su kira aikin gayya domin kwashe sharar.


Bajare ya yi wannan kalami ne a lokacin da yake tattaunawa da Managarciya kan matsalar sharar da yanda ya damu kwarai, ganin yanda aka ki baiwa sharar muhimmanci duk da hatsarin kamuwa da cuta da annoba a yankin, ya ce muna sanar da gwamnati bayan sati biyu matukar ba ta kwashe sharar ba za mu kira aikin gayya a fadin jihar duk wanda yake da wani abu da zai taimaka ya zo, don a kawar da sharar daga wurin, mutane su samu iska mai lafiya a jiki.


"Idan wa'adinmu ya cika ba a kwashe ba, za mu nemi da gwamnati ta gaya mana wurin da za mu zuba sharar bayan mun kwashe ta, don kaucewa laifi, mu zuba a bayan gari ta ce ba a can ne take so ba, ko mu rika kaiwa manoma a gonakinsu ta ce ba haka ta so ba, kan wannan aikin muna son a bi ka'idar gwamnati don ba fada muke da ita ba, muna son bayar da tamu gudunmuwa ne ga abin da muke ganin an kasa", a cewar Bajare.


Ya ce ba daidai ba ne a zuba ido ana kallon mutane suna cutuwa kan abin da in an hada kai ana iya kawar da shi, sharar nan ta addabi mutanen unguwar nan matuka ta kawo masu ci baya a haujin tattalin arzikinsu da lafiyarsu, duk wannan ya faru kan sakaci na gwamnati, don haka muka shirya abin da ya dace kan sharar nan.


"Ina kira ga gwamnati ta bamu hadin kai bayan sati biyu in ba ta kwashe sharar nan ba, ta sanar da mu in da zamu kai sharar don a kai, kar ta yi la'akari da bambancin jam'iya aikin al'umma na kowa ne ba sai gwamnati kadai ba", in ji Malami Bajare.