Tambuwal ya aminta da rushe ƙauyen da ya zama maɓoyar ɓatagari a Sakkwato

Tambuwal ya aminta da rushe ƙauyen da ya zama maɓoyar ɓatagari a Sakkwato
Tambuwal ya aminta da rushe ƙauyen da ya zama maɓoyar ɓatagari a Sakkwato
 
Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya aminta da roshe ƙauyen da ya zama maɓoyar ɓatagari a Sakkwato domin a yi wani abu da zai amfani jihar.
Gwamnan a ziyarar da ya kai wurin domin gani da ido tare da jami'an gwamnati ya sanar da hakan.
Ya ce kwamitin majalisar tsaro ta bayar da shawara a roshe wurin kuma da zaran sun kammala rahotonsu aka gabatar zai aminta da roshe wurin domin samar da wani abu da zai amfani mutanen jiha.
Gwaman ya ba da umarnin a tantance mazauna wurin nagari daga cikinsu a samar musu wasu wurare su koma batagarin kuwa a hukunta su.
Tambuwal na tare da rakiyar shugabanin jami'an tsaro a jihar Sakkwato da wasu mukarabansa. 
 
Remon Vilage  Kauye ne da  wani Inyamuri tsohon soja  ya kafa garin duk da ya samu wasu mutane Hausawa a gefensa.
 
 Raymond Villag tashin hankalin dake tattare da wannan wurin  babu abinda ba'a aikatawa a cikinsa, da suka kunshi shaye-shayen Kwayoyii da wiwi. Sannan wasu mata  da ake nema sama da kasa sun bace idan aka je can ana iya ganinsu.
 
A takaice dai wannan Kauye na RAYMOND VILLAGE ya ba da gagarumar gudun mawa wajen lalacewar tarbiyyar'ya'yan musulmin dake birnin Sokoto da kewaye musamman mutanen dake Makwabtaka da wannan wurin.
 
Irin wadann wurare ke zama mabuya ga 'Yanta'addan Bindiga, Kidnappers, da Armed Robbers da sauran masu aikata manyan laifuka. 
Wannan bayani na Gwamna Tambuwal zai faranta ran mutanen Sakkwato ganin wani aikin jihadi ne ya yi ga damar da Allah ya ba shi.