Sojoji sun kashe kwamandan ƴan bindiga Mai suna Ɗan Ɗari Biyar a Sakkwato
Dakarun rundunar sojin Najeriya da ke ƙarƙashin Operation FANSAN YANMA sun samu nasarar kashe fitaccen shugaban ƴan bindiga mai suna Dan Dari Biyar, a wani samamen kakkabe su da suka gudanar a yankin yammacin ƙaramar hukumar Sabon Birni, Jihar Sakkwato.
Wata majiya mai tushe daga hedikwatar rundunar soji ta tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa an kashe Dan Dari Biyar ne a ranar Alhamis, yayin da yake ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa daga dangin waɗanda aka sace a dajin da ke tsakanin kauyukan Turtsawa, Mazau da Zango.
Majiyar ta bayyana cewa Dan Dari Biyar ya yi fice wajen zaluntar waɗanda ya sace, yana nuna musu rashin mutunci kafin ya buƙaci kuɗaɗen fansa masu yawa.
An gano cewa yana da mafaka ne a cikin dajin Tidibale, daga inda yake shirya kai hare-hare a yankunan Lalle, Tsamaye da sassan Gwaronyo. Haka kuma, an danganta shi da kone kauyen Gidan Sale da ke gefen Gundumi.
Binciken leƙen asiri ya nuna cewa Dan Dari Biyar na da hannu a hare-hare da dama, kwanton-bauna da kona gidaje a yankin gabashin Sakkwato, musamman a wuraren da ke cikin dazuka masu wahalar shiga.
Samamen da ya kai ga kisan shugaban ƴan bindigar ya samu ne tare da haɗin gwiwar dakarun sojin Najeriya da masu tsaron al’umma da ke ƙarƙashin shirin gwamnatin jihar Sakkwato na kare al’umma.
A yayin samamen, an kwato makamai, harsasai da na’urorin sadarwa daga maboyar ‘yan bindigar, yayin da ake ci gaba da farautar sauran mambobin ƙungiyar da suka tsere.
managarciya