Gwamnan Sakkwato Ya Gana da Shugabannin Tsaro Kan Harin da Yan Bindiga Suka Kai 

Gwamnan Sakkwato Ya Gana da Shugabannin Tsaro Kan Harin da Yan Bindiga Suka Kai 

 

Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya kira taron majalisar tsaro na gaggawa ranar Litinin domin tattauna batun da ya shafi harin 'yan bindiga wanda ya ci rayukan mutane 37 ranar Asabar a arewacin jihar. 

Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun kai kazamin hari kan mazaunan kauyuka uku a yankin ƙaramar hukumar Tangaza da wasu kauyuka biyu a yankin Gwadabawa.
Ƙauyukan da mummunan harin ya shafa sun haɗa da Raka, Raka Dutse da kuma Filin Gawa, inda maharan suka kashe rayuka 37, wasu da yawa suka ji raunuka. 
Gwamna Aliyu, wanda ya katse tafiyar da ya yi zuwa Abuja kan harin, ya lashi takobin hana 'yan bindiga da sauran yan ta'adda sakat a Sakkwato. 
Da yake jawabi ga yan jarida bayan kammala taro da shugabannin hukumomin tsaro da yammacin Litinin, Kakakin mai girma gwamna, Abubakar Bawa, ya faɗi wasu daga cikin abinda aka tattauna. 
Ya ce daga cikin batutuwan da taron ya tattauna a kai shi ne lalubo yadda za'a gina dangantaka da jituwa a tsakanin hukumomin tsaro a jihar. 
"Domin ta haka ne kaɗai za'a samu danganta mai kwari tsakanin jami'an tsaro da kuma ƴan banga a kokarin kawo karshen 'yan bindiga," inji shi. Gwamnan ya kuma koka kan ayyukan Imfoma waɗanda a ganinsa ya kamata a tashi tsaye don kawo ƙarshensu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Bugu da ƙari, gwamnan ya yi alƙawarin biyan bashin alawus ɗin watanni 5 wanda dakarun rundunar sojin Operstion Hadarin Daji suka biyo gwamnatin jihar. 
Haka zalika ya ce gwamnatinsa zata yi kokarin magance sauran kalubalen da rundunar take fuskanta domin ta ci gaba da aikin yaƙar yan ta'adda. Daga karshe, ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu kan ya yi Addu'ar Allah ya saka musu da mafificin sakamako watau Aljanna.