Saraki ya bukaci a gaggauta janye sabon harajin kaso 4% na kaya
Saraki ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta sake duba harajin da ake shirin sakawa, ya ce zai cutar da ‘yan kasuwa da masu sayan kayayyaki.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya nuna damuwa kan aiwatar da sabon harajin kashi 4% na Free-On-Board (FOB) da Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta bullo da shi.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, Saraki ya yi tambayoyi masu mahimmanci, yana mai gargadin cewa sabuwar dokar za ta jefa ‘yan kasuwa da masu amfani da kayayyaki cikin matsala.
"Da la’akari da cewa ana shigo da kayayyaki da kudin da ya kai Naira tiriliyan 71 a kowace shekara, wannan sabon harajin kashi 4% zai kai Naira tiriliyan 2.84. Shin hakan yana nufin cewa Hukumar Kwastam na bukatar karin Naira tiriliyan 2.84 kowace shekara domin gudanar da ayyukanta?"
"Kada a manta, su ma suna da kasafin kudi kuma suna karbar wani kaso daga kudaden haraji da suke tarawa."
Saraki ya caccaki yawan kashe kudi a Hukumar Kwastam
Saraki ya kuma soki yadda NCS ke ci gaba da kara yawan kudaden da take kashewa, yana mai nuna cewa yanzu suna kokarin kashe fiye da dala biliyan 1.5 a kowace shekara, duk da cewa kasar na fama da matsalar talauci da rufe harkokin kasuwanci da yawa.
"Ba makawa, ‘yan kasuwa za su mayar da wannan karin haraji kan masu saye, wanda hakan zai kara matsin lamba ga miliyoyin iyalai da ke fama da wahala."
Ya ce sabon harajin ba kawai ya shafi kayayyakin alfarma ba, har da duk wani abu da ake shigowa da shi daga waje, ciki har da masana’antu da ke shigo da kayan sarrafawa.
"Misali, idan masana’antu na shigo da kayansu da harajin kwastam na kashi 5% ne kawai, yanzu Hukumar Kwastam za ta karbi karin kashi 80% na wannan kudin harajin a matsayin kudin gudanarwa. Ta yaya hakan zai taimaka wajen saukakawa kasuwanci?"
Saraki ya bukaci gwamnati da ta janye harajin
Saraki ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta sake duba dokar kuma ta dakatar da aiwatar da ita, yana mai gargadin cewa idan aka ci gaba da aiwatar da sabon harajin, zai cutar da al’ummar Najeriya.
A ranar 5 ga Fabrairu, Hukumar Kwastam ta sanar da cewa za ta fara karbar harajin kashi 4% kan FOB na duk wani kaya da aka shigo da shi.
Hukumar ta ce wannan mataki yana bisa tanadin dokar Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCSA) ta shekarar 2023.
managarciya