'Yan Bindiga Sun Baiwa Gari 10  Wadin Biyan Tara Ko Su Afka Masu A Sakkwato

'Yan Bindiga Sun Baiwa Gari 10  Wadin Biyan Tara Ko Su Afka Masu A Sakkwato
 
 

Mahara dake cin karensu ba babbaka a yankin karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato  sun bayar da umarni da sharadin mutanen kauye 10  su biya tarar kudi kafin wannan jumu'ar ko kai masu hari.

Mutanen wuraren sun daina  fita gona har sai an kammala hada kudaden gudun kar a kai masu farmaki da yawan mutane suna kokarin biyan kudin don kacewa farmakin.

Wanda ya yi magana da manema labarai ya ce 'yan bindigar suna la'akari da yawan gari da kasuwancinsa a wurin saka kudin fansar na hana kai masu hari.  
"Subhanallah yanzu haka duk kauyukan dake yammacin karamar hukumar Sabon Birni 'yan bindiga  sun aza musu kudi ga garuruwan kamar haka:kwatsal 4,000,000, Masawa 5,000,000, Dogon marke 2,500,000, Kuzari 500,000, kaifin aska 1,0000,000, Gomozo 1,000,000, Dakwaro 3,000,000, Kwaren Gamba 4,000,000, Kuka 1,000,0000, Allakiru 2,000,000.
"Wasu sun biya wasu Kuma ana hadawa, a tsarin da aka kawo magidanta sukan bayar da 2000 matasa su bayar da 1000 kowanensu," a cewarsa.
Ya ce Maharan sun bayar da ranar Jumu'a ta wannan sati ya zama ranar karshe ta biyan kudin gudun kawo hari a garuruwan.
Dan Majalisar dokokin jihar dake wakiltar Sabon Birni Almustapha Gobir ya tabbatar da lamarin ya ce kan wannan amincewar da mutane suka yi an dakatar da kai hare-hare a yankin.
"Mutane sun amince su biya kudin a barsu cikin zaman lafiya da su dogara da jami'an tsaron kasa amma su tafi gudun hijira," a cewarsa.
Tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni Idris Muhammad Gobir yana ganin biyan tarar da mutanen ke yi ba zai samar da mafita ba domin maharan na da kungiyoyi daban-daban babu tabbaci in ka biya wadan nan wasun ba za su kawo maka farmaki ba.
Ya ce hakan ya faru a garin Gatawa da Tarah aka sace mutane aka kai kudi wadanda suka sace mutanen suka ce ba su ba ne aka baiwa.
Kokarin magana da kwamishinan tsaro na jihar Sakkwato Kanal Garba Moyi ya ci tura.