Ba wata rashin jituwa ko fada a tsakanin mu da gwamnati-----Sarkin Musulmi 

Ba wata rashin jituwa ko fada a tsakanin mu da gwamnati-----Sarkin Musulmi 

 
 
Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya yi kira ga al'ummar musulmi su cigaba da yiwa shugabanni addu'a domin samun nasara a tafiyar da jama'a.
Alhaji Sa'ad a a jawabinsa na barka da Sallah da ya gabatar ga al'ummar musulmi a fadarsa, Lahadi ya ce karantarwar addini da aka samu a watan Azumi mai albarka abu ne da ya kamata a rike a sanya cikin aiki.
"Mu kara daure damara kar mu koma gidan jiya waton aiwatar da sabon Allah mu dage da yin ibada kar a ja baya. Sannan mu rika yiwa shugabanni addu'a.
"Ku kuma shugabanni ku ji tsoron Allah cikin shugabanci in za a yi aiyukkan jama'a kar a ji tsoron kowa sai Allah," kalaman Sarkin Musulmi.
Da ya juya kan dangatakarsa da gwamnatin Sakkwato ganin yadda ake ta yada jita-jitar akwai tsamin danganta a tsakaninsu wanda hakan ya sa gwamnatin da ta shigo ta sauke wasu sarakuna da sarkin ya naɗa ta kuma yi gyaran fuska kan dokar masarauta wanda aka zargi Sarkin ne aka yi yunkurin tsigewa ya ce "ba wata rashin jituwa ko fada muna aiki tare a koyaushe aikinmu mu taimakawa gwamnati(Sakkwato) ga shiraruwan da ta dauko don ciyar da jama'a a gaba."
Sarki ya yi kira ga jami'an tsaro su kara kaimi a matsalar tsaro tana da saura a ko'ina ba Sakkwato kawai ba.