Fargaba ta mamaye garuruwa hudu da 'yan bindiga suka aikawa takarda a Sokoto

Al'ummar garuruwan Kwanar Kimba, Rikina, Dange da Shuni, sun samu takardar kai misu hare-haren ta'addancin ne a wata wasika da ake zargi 'yan ta'addar ne suka lakata a jikin wani icce a Kwanar Kimba.

'Yan bindiga sun rubutawa wasu garuruwa 4 dake cikin karamar Dange-Shuni  Kilomita daya daga birnin Sokoto wasikar kai musu hare-haren ta'addanci daga yanzu zuwa kowane lokaci.

Al'ummar garuruwan Kwanar Kimba, Rikina, Dange da Shuni, sun samu takardar kai misu hare-haren ta'addancin ne a wata wasika da ake zargi 'yan ta'addar ne suka lakata a jikin wani icce a Kwanar Kimba.
 
A cikin wasikar, 'yan bindigar sun bayyana ko jami'an tsaro miliyan daya gwamnatin jihar Sokoto za ta jibge a wadannan wuraren sai sun kai hare-haren da suka shirya kaiwa.
Fargaba da tsoro ya mamaye mutanen garuruwan duk da ba a san gaskiyar takardar ba.
Wakilinmu ya tuntubi jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Sakkwato ASP Sanusi Abubakar ko suna da masaniya kan takardar ya ce zai bincika ya sanar da Managarciya, har zuwa wallafa labarin bai kira ba.