PDP Ta Sa Ranar Da Za'a Sake Zaɓen Fidda Gwani A Katsina

PDP Ta Sa Ranar Da Za'a Sake Zaɓen Fidda Gwani A Katsina

Ruhotanni sun tabbatar  jam'iyyar  PDP ta kasa ta sake sanya ranar da zata gudanar da Zaɓen Fidda Gwani a Katsina, Lagos, Imo, Benue. 

Kamar yadda Jaridar Katsina Post ta wallafa jam’iyyar PDP ta amince da sake gudanar da Zaben Fidda Gwani a Jahohin Lagos, Imo, da Benue, da Katsina.

A cikin wata sanarwa da mai kula da harkokin Jama’a na PDP Debo Olugunagba ya Fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa Jam’iyyar ta ɗauki wannan matsaya bayan yin karatu akan rahoton da Kwamitin Zaɓe da na Ɗaukaka Ƙara suka shigar a Jahohin.

Wuraren da aka amince a sake zaɓen fidda Gwani sun hada da Mazaɓar Ahiazu da ta Orsu a Jahar Imo, zai wakana a ranar 5 ga watan yunin Shekarar 2022.

Majiyar dai kara da cewa zaɓen Fidda Gwani na Ɗan Majalisar Wakilai ta Ƙasa na Lagos (Mazaɓu 24) za’a gudanar dashi a ranar Litinin 6 ga watan Yuni na Shekarar 2022.

Sanarwar tace “Zaɓen Fidda Gwanin Dan Majalisar Dattijai na Kaduna ta Tsakiya, da Enugu ta Yamma, da Ɗan Majalisar Wakilai na Boki/Ikom, da Yakuur II dukkanin su a Jahar Cross River da aka sanya za’a gudanar a ranar 4 ga watan Yunin Shekarar 2022 an soke shi.

Dukkanin Ƴan Jam’iyyar da lamarin ya shafa ana kira a garesu dasu san da haka

©Katsina Post