ANA BARIN HALAL...: Fita Ta 51

ANA BARIN HALAL...: Fita Ta 51

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe

Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

Idan kana/kina sha’awar:

_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._

_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._

_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._

_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._

_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
*Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t

*Page 51*


*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE  ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559


~_______
Jiki a sanyaye na ajiye kwalban turaren a inda na ɗauko shi kan mirrow,  rigan bacci na kawai na ɗauko nasaka, duk abinda nakeyi idon shi na biye da ni,  ina gamawa ya miƙo mun hijab ɗin da nake sallah da shi, jiki na a sanyaye na saka, sannan ya miƙo mun socks ɗina na saka.

Sallah ya jamu raka'a biyu, bayan mun idar ya mana dogon addu'a na zaman lafiya, nidai Ameen nake bishi da shi, daga nan ya ɗauko mana cooler da wani cocounut juice mai cike da ƙamshin flavour da madara,  duk yadda naso ƙin cin naman kazan da akayi shi kaman danderu, amma bai barni ba sai da naci, a baki ya dinga bani har na ƙoshi,  daga nan na shige toilet na wanko bakina sosai, bayan na fito na samu ya kwashe kayan zuwa kitchen.


Gado na hau na ja duvet na rufu, ko minti biyar ban cika ba ya shigo,  ina jin shi yana tambayan yaya na rufe har kaina,? Nidai shiru ban amsa mishi ba, kashe wutan ɗakin yayi ya kunna bedside lamp, a haka ya hawo gadon yana jawo ni jikinshi,  "Eeshan A.G shine baki jirani ba"? 

Nidai bance komai, wayan shi aka ƙira ina ji yaja tsaki ya katse wayan, murya chan ƙasa yana mitan, "kaji mun munafukin yaro, kagama angwancewa tun shaiɗan yana saurayi, ni yanzu da nake niyyah zaka wani dameni da ƙiran tsakar dare",  ya faɗa  yana jan tsaki, nidai dariya ne naji yazo mun,  ban shiryah ba ya kubce mun, shima ina jin shi yayi dariyan kaɗan ya kwanto a jikina.

Fuskanta cike da murmushi tana wani lumshe ido ta dubeni,  "Aunty nice a wannan daren ne alama ya nuna nasamu lafiya, domin kuwa a wannan rana mai cike da tarihi, aminci, ƙauna, amana, da kuma soyayyah,  A.G ya karɓi darajana da ƙima na, wanda wannan wata rana ce da bazan taɓa mantawa da shi ba a tarihin rayuwata,
Dare ne daya ƙullah abubuwa masu girman gaske a rayuwata da  A.g,  dare ne mai haske wanda ya haska duniyar mu da A.G, a wannan daren nagama zama A.G shima yazama Eeshaa",  kallona tayi fuskan ta cike da farin ciki, sannan ta cigaba,   "Allah sarki  A.G wato ranan naga rawan jiki da ƙauna, don a wannan daren ya mun alƙawarin mota, kuma haka akayi, washegari kuwa ko idon shine ya rufe, yana idar da sallah ya ƙira mummy a waya, wato nidai naga takaina a wannan rana, don tana ɗauka kuwa yace,  "mummy wallahi beauty ta warke, inaga gobe tare ma zamu tafi Abujah da ita",  duk sai naji kunya ta lulluɓe ni,  ballantana da tace mishi tana zuwa idan gari ya ƙarasa washewa.

Nidai dawowa nayi kaman wata sarauniya, don komai shiya mun, yadda kika san babu wata mace a duniya bayan ni,  wato Aunty nice naga so, ƙauna, kulawa a rayuwar A.G,  haka yayi komai ya gyara ni ya gyara ɗaki, wuraren ƙarfe 10:00am kuwa sai ga mummy, kayan breakfast ta haɗu mana rinkicicif, ga peppesoup Ɗin kaza daya sha kayan ƙamshi na gargajiya, haka dai itama ta lalace a tarairaya na, ga tonun sili da suka mun, don wallahi sai da ta ƙira ummie ta zayyane mana lafiya ya samu, ita dai ummie murmushi ne nata da hamdala, mummy day sai da akayi sallan magrib ta bar gidan, bayan ta zayyana mishi Dadda tace babu inda zanje sai na ƙarasa magani na, kuma haka babu yadda ya iya, dole da zai tafi ya mayar dani, da zai tafi ƙin sake fuska yayi, ya haɗe kaman A.Gn da dana sani, don ko ni banga fuska ba ranan, ko da ya isa yaƙi ƙiran kowa, sai nice ma ya turo mun msg ya sauƙa lafiya, nima reply na mishi da Alhamdulillah na barshi.


Humm ranan friday sai ga Gwani A.G kam ya dawo bauchi, baki mummy ta riƙe tana kallon shi cike da mamaki, sharewa yayi kaman bai san me yake faruwa ba, daga nan kuwa ya shige ɗakin mummy inda nake kwance ina waya da Hadiza, ganin shi tsaye a bakin ƙofa ya ƙura mun ido yasaka na tashi zaune ina sallama da hadiza.


Ido na ƙura mishi ina kallon shi, shima idon ya zuba mun yana kallo na,  "ki shiryah idan kin gama kallona ɗin mu wuce gida" ya faɗa yana wani harara na,  dariya ma yabani ,   "nikan don Allah ka barni anan, bansan me zan iya gayawa mummy ba, ae zataga kaman bamu da kunya",  na faɗa ina maida kallona ƙasa, don ganin irin yadda ya ƙura mun ido,  hmmm naji yace, sannan ya matso ciki har bakin gadon ya tsaya,  "anan kenan kike ga yakamata mu kwana ko"? Ɗaga kafaɗa yayi alaman babu komai hakan,  "shikenan bari na sauƙe kayana sai mummy ta bamu wuri mu kwana anan".


Jin abunda yace yasaka na wani zaburo nace,  "yayah kuma mu kwana tare da kai a ɗakin mummy? ae ko gidan nan bai kamata mu kwana tare ba ballantana kuma a ɗakin mummy",  na faɗa ina sauƙowa da ƙafufuwana ƙasa.


"Tunda kinga hakan bai dace ba sai ki tashi baki alaikum mu wuce inda ya dace da mu, don wallahi yau babu wanda ya isa hanani kwana ɗaki ɗaya gado ɗaya da ke"........ Bai gama ba kuwa mukaji muryan mummy tace,  "babu kam Barrister, ke kuma Ayshaa ɗauki kayanki ku wuce, kafin ya nuna mun shi baijin kunyan kowa, kedai ki kula da magungunan ki kinji ko",  ta faɗa tana juyawa ta bar ɗakin,  kunya naji ya rufe ni, duban shi nayi kaman zanyi kuka nace,  "haba mana A.G",  hararana yayi yace,  "kin tashi ko sai na ɗale gadon"?

Tashi nayi ina ƙunƙuni ƙasa-ƙasa na zuba magunguna na a wani leda, banda shi ban ɗauki komai ba sai handbag,  ko sallama banyiwa mummy ba, don ta wuce parlon daddy duk da baya nan, shi kaɗai yaje yayi mata sallama, a tsaye a bakin mota ya sameni,  kashe mun ido yayi bayan ya ɗaga mun giran shi duka biyu, nidai kunya ya bani na juyar da kaina kawai na shige motan.

A gidan mu nida shi muka gyara gidan, naso ɗaura a binci amma fir yaƙi barina,  dole mukaje *MCDOWALS* muka sayo snacks, sai kaza gashin injin da yogouth,   haka ranan ma muka lalace da nunawa juna ƙauna, wannan daren ma darene mai girma a wurin A.G, mun nunawa juna so da ƙauna, kulawa da A.G ya nuna mun har sai da naji kaman babu yani a duniya, ranan monday ya sake juyawa ya koma Abuja, ni kuma na koma gida wurin mummy.

**********
Bayan 2month jiki yayi sauƙi sosai, sai lokacin mukayi shirin tafiya tare da A.G, satin da yazo ummie ta ƙirani inda hali na tambayi A.G nazo na duba jikin sabeer, domin yau sai da aka ɗaura mishi drip,  hankalina a tashe da yazo na gaya mishi, kuma ana sallan magrib muka wuce gidan mu, muna shiga kuwa muka haɗu da su suna shirin wucewa asibiti da shi, duk sabeer ɗina ya fige yayi baƙi, hankali atashe muka bi bayansu akaje asibitin, *ALWADATA* wani private hospital na yara da yake Fadaman mada mukaje, muna asibitin har 10:00 na dare ana abu ɗaya, sai da mukaga an bsu ɗaki har an saka mishi drip yana bacci tukun muka tafi, duk zuciyata babu daɗi muka dawo gida.


Ƙarfe shida bayan mun gama azkhar munyi karatun qur'an, sai ga wayan ummie ta ƙirani, wani irin faɗuwan gaba sosai naji ya kamani, amma na daure na ɗauka, bakina yana rawa na gaida ummie,  "Ayshaa"  naji ummie ta ƙirani a hankali, da ƙyar na amsa mata, tambayana yyh A.G yake tayi, shima amsa mata nayi da yana lafiya, sannan cikin lumana da nasiha take gaya mun Allahn da yafi mu son sabeer ya karɓi abunshi, idan A.G ya amince nazo kafin a kaishi,  kuka sosai na fashewa ummie da shi, wanda tayi sauri ta kashe wayan,  da sauri A.G ya matso jikina ya rungumeni, bai tambayeni komai ba don volume ɗin wayana daya ke bayyane ya kai mishi komai, rarrashi na yakeyi har zuwa wasu mintuna, sannan yace na tashi na sake wanka muje, shima ɗakin shi ya wuce yayi wanka, bayan nayi wanka na saka dogon rigan atamfah ta soso, sannan na ɗauko hijab green kalan atamfar na saka, sai ga A.G ya shigo da cup ɗin tea a hannun shi,  babu yadda na iya haka ya takura ni sai dana sha half na tea ɗin tukun muka tafi gidan mu,  duk illahirin ƴan gidan s]na parlon mamie, gaban ummie naje na zauna n kwantar da kaina a kan cinyanta ina kuka, tabbas naji mutuwar Ɗana sabeer, amma babban damuwa na na rabu da wani abu daya danganci habiba, don mutuwar habiba ne najishi ya dawo mun, kaman yau akayi rasuwan nakeji.

Ko kunya mutane mamie bataji ba lokacin da Aliyu da maman shi suka zo da ƴan'uwan shi, haka ta dinga fade -faɗen magana ana hana ta amma batayi shiru ba, har Allah ya isa saida ta musu, amma da yake mummyn Aliyu tafita bariki ko bin ta kanta batayi ba, ɗaukan gawan jikanta tayi ta mishi addu'a, shima Aliyu addu'a yayi mishi sosai yana share hawaywn shi, gefe ɗaya kuma amaryar shi tana zaune cikin ƴan'uwan shi, har ita mamie bata bari ba ta zage ta tsaf,  lokacin da suka gama kuwa suka ɗauki gawan yaronsu suka gita domin ayi mishi sallah, lokacin kuwa Aunty Rakiya ne ta mata jan ido ta nuna mata bata isa ba sue da ƙarfi akai,  gashi gida babu Abba babu mazajen gidan, mudai munga fitina da tashin hankali ranan, don ƙarshe sai da sukayi uwar watsiya da Aunty Rakiya da Mamah, don da abun yafara tsamari wai Abba yace tunda A.G yana gidan ya tsaya akan komai kafin su iso, ai kuwa inda ta shiga bata nan take fita ba, shine su mamah suka taso mata, don tana farawa ummie ta jani muka fice,  hajiya ummah sai da ta kusan tsine mata albarka ranan, nidai ban sake komawa ba sai da zamu tafe A.G yajani muka shiga, nan ma sai da ta gaya mana abunda banji daɗi ba, ina ankare da A.G duk sai mamakinta yake tayi, jiki na a sanyaye uka wuce

Washe gari kuwa Abba da yayah muhammad suka zo, kacha -kacha Abba yayi mata ka yace kowa ma ya watse a zaman, kuma ya ƙira Raliya da itama ranan tazo yayi mata kacha-kacha yace kuma ta juya ta tafi, nima ya mana sallama da A.G yace mu wuce Abuja baice mu zauna ba haka ya isa, abarta da halinta, Allah yaga yaron jinin habiba ne, baida hakkin girban ayyukanta shiyasa Allah ya ɗauke shi batare da ya girma ya girbi baƙin ciki ba

Don Allah kuyita haƙuri dani dai

*AUNTY NICE*