Majalisar Dunkin Duniya Ta Bayyana Irin Matsalolin Da Cire Tallafin Man Fetur Ya Jawo A Nijeriya
Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta bayyana yadda yunwa ke kara yawa musamman a Arewacin Najeriya saboda cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi. Wakilin majalisar ta bangaren kawo dauki a Najeriya, Matthias Schmale shi ya bayyana haka a ranar Laraba 28 ga watan Yuni.
Schmale ya ce akalla yara 700,000 ne 'yan kasa da shekara biyar ke fama da matsanancin yunwa a kasar, Legit.ng ta tattaro.
Ya ce wadannan yara na daga cikin mutane miliyan 4.3 da ke jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa da suke fuskantar matsananciyar yunwa.
"Na taba zuwa jihar Borno da sauran jihohin guda biyu sau da dama, naga yadda iyaye mata ke fama da 'ya'yansu wadanda ke cikin 'ynwa a hukumomin tallafawa matsalar 'yunwa."
Schmale ya gargadi cewa wannan bala'i ya samu ne saboda tsawon shekaru da aka yi ana fama da rashin tsaro a yankin, wanda ya hana mutane da dama zuwa gona don samun abinci. Ya kara da cewa matsalar da rashin tsaron ta kawo akwai sauya yanayi da ya jawo ambaliyar ruwa wanda ya shafi mutane fiye da miliyan hudu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa a wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ya nuna cewa Arewa maso Gabas sun karbi kashi 25 daga cikin $1.3bn da aka bayar.
Sai dai matsalolin takin zamani da abinci da kuma babbar matsalar cire tallafin mai shi ya kara rikirkita al'amarin.
A wani labarin, masu sana'ar POS sun bayyana sabon farashin cire kudi da turawa. Kungiyar masu wannan sana'a ce reshen jihar Lagos ta bayyana haka ganin yadda aka cire tallafin man fetur.
Kungiyar ta ce farashin na iya yin kasa duba da wurin da mutum yake, amma saba doka ce yafi sabon farashin da aka saka.
managarciya