Ahmad Lawan Yayi Canje-Chanjen Shugabancin Kwamitocin Majalisar Dattawa

Mai taimaka ma shugaban majalisar dattawa akan aikin jarida Ezrel Tàbiowo ya bayyana hakan a wata takardar manema labarai da ya fitar.
Yace yanzu, Sanata Sahabi Alhaji Ya’u ne shugaban kwamitin majalisar akan hukumar kidaya ta kasa da hukumar samar da katin dan kasa, sai Sanata Adetokunbo Abiru a matsayin shugaban kwamiti akan masana'antu da Sanata Saidu Alkali, shugaban kwamitin majalisar akan ciniki da zuba hannun jari, da kuma Sanata Kabiru Barkiya a matsayin shugaban kwamitin hulda da majalisun dokoki.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya sanar da canje-canje a shugabancin wasu daga cikin kwamitocin majalisar.
Lawan ya bada sanarwar ne jim kadan kafin majalisar ta dage zamanta zuwa 9 ga watan Oktoba don bai wa kwamitocin ta damar aiki akan kasafin kudin 2022.