Wasu Gwamnoni Arewa Sun Rinƙa Jin Haushina  Don Na Gina Makarantun Allo----Inji Jonathan

Wasu Gwamnoni Arewa Sun Rinƙa Jin Haushina  Don Na Gina Makarantun Allo----Inji Jonathan

Tsahon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya ce wasu gwamnoni a Arewa ba su ji dadin yadda ya gina makarantun Allo ba wato tsangayoyi a arewacin Nijeriya ba. 

Ya bayyana hakan ne a wani taron akan yadda za'a magance matsalolin tsaro dake addaban arewacin Najeriya dama fadin Najeriya baki daya wanda aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja jiya Alhamis, inda ya bayyana cewa mun gina makarantun Allo kusan 35 a arewacin Najeriya amman a halin yanzu duk anyi watsi dasu, inda ya roki gwamnoni dasu kula da nauyin da yake kansu na hakkokin jama'an da suke mulka.

Ya kara da cewa ya kamata Gwamnatin jihohi su gyara tsarin karatun Tsangaya zuwa na zamani kamar yadda aka inganta na Boko, 

Tsohon shugaban Kasar Jonathan ya kuma rokon gwamnonin dasu kara kokari don ganin sun kula da sha'anin makarantun Tsangaya a jihohin su tare da daukar nauyin karatun su zuwa mataki na gaba.

Daga Babangida A Maina