Gwamnatin  Najeriya Ta Ƙaddamar Da Ingantaccen Tsarin Fasfo A Yanar Gizo

Ministan a ma'aikatar harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya ƙaddamar da tsarin ofishin jekadancin Nijeriya dake London ya ce nan ba da jinawa ba za a soma aikin bayar da fasfon mutum yakan cika koma daga baya ya zo ofishin hukunar shige da fice ta ƙasa domin ɗaukar yatsun hannunsa. Ya ce wannan tsarin zai taimakawa tsaron ƙasa musamman ba wata ƙasa da ke da tsari saman na Nijeriya. Ministan ya ƙara da cewar sun samar da Fasfo sama da miliyan biyu a cikin shekara biyu ga 'yan Nijeriya a dukkan duniya.

Gwamnatin  Najeriya Ta Ƙaddamar Da Ingantaccen Tsarin Fasfo A Yanar Gizo
 
Daga Abbakar Aleeyu Anache. 
 
Nijeriya ta kaddamar da ingantaccen tsarin fasfo  ta yadda za a rika yin harkokin fasfo ta yanar gizo, domin samar da inganci da  saukaka tsarin neman fasfo ga 'yan Najeriya  a cikin gida da waje.
 
Dama an dade ana kai ruwa rana a game da matsalolin nema ko sabunta fasfo a ofisoshin hukumar kula da shige da ficen Najeriya da ma ofisoshin jakadancin kasar a waje, in da yan kasar da dama ke kokawa a kan tsawon lokacin da ake dauka wajen samu sabon fasfo ko sabuntawa, zargin ma'aikata da rashin gudanar da aiki yadda ya kamata, zalinci a wajen aiki da dai sauransu, ana ganin fito da wannan tsari zai kawo karshen lamarin.
Ministan a ma'aikatar harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya ƙaddamar da tsarin ofishin jekadancin Nijeriya dake London ya ce nan ba da jinawa ba za a soma aikin bayar da fasfon mutum yakan cika koma daga baya ya zo ofishin hukunar shige da fice ta ƙasa domin ɗaukar yatsun hannunsa.
Ya ce wannan tsarin zai taimakawa tsaron ƙasa musamman ba wata ƙasa da ke da tsari saman na Nijeriya.
Ministan ya ƙara da cewar sun samar da Fasfo sama da miliyan biyu a cikin shekara biyu ga 'yan Nijeriya a dukkan duniya.
Muƙaddashin babban  kwanturola na hukumar a ƙasa Isah Jere ya ce a Nijeriya ne aka fara fasfo a yanar gizo dukkan ƙasashen Afirika a shekarar 2007.
Ya roki dukkan 'yan Nijeriya dake riƙe da fasfo su zama jekadu nagari ga Nijeriya.