Neman Adawo Da Tallafin Mai: Masu Zanga-Zanga Sun Ɓalle Ƙofar Majalisa
Masu zanga-zangar cire tallafin mai da ƙungiyoyar ƙwadago ta kasa (NLC) ke jagoranta sun ɓalle ƙofar shigar majalisar dokoki ta ƙasa.
Rahotanni sun nuna fusatattun masu zanga-zangar ta NLC da takwararta TUC sun balla kofar shiga majalisar ne bayan takaddama da jami’an tsaro da ke gadin harabar majalisar.
Sun isa wurin ne bisa jagorancin shugaban NLC Joe Ajaero da takwaransa na TUC Festus Osifo, inda suka bukaci jami’an tsaron sun bude musu domin su shiga su gabatar da korafinsu, amma jami’an tsaro suka ki.
Ana cikin haka ne ’yan kungiyar suka yi kukan kura suka karya kofar suka kutsa cikin harabar majalisar da karfin tuwo.
~ Aminiya
managarciya