Gwamnatin  Kebbi Ta Tallafawa Iyalan 'Yan Sakan Da Suka Rasa Rayukansu Ya Yin Artabu Da 'Yan Bindiga

Gwamnatin  Kebbi Ta Tallafawa Iyalan 'Yan Sakan Da Suka Rasa Rayukansu Ya Yin Artabu Da 'Yan Bindiga
 
Daga Abbakar Aleeyu Anache. 
 
Gwamnan jihar kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya Tallafawa Iyalan 'yan Sakan da suka rasa rayukansu ya yin artabu da yan bindiga ta hannun shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru Hon Bala Mohammed Isah Gajere,
 
A nasa jawabin shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru Bala Gajere ya ce gwamnan jihar kebbi ya nuna rashin jin dadinsa bisa kisan gilla da aka yi wa wasu yan Sa'kai da suka hada da shuwagabanninsu tare da yaransu
 
Da yake martani kan lamarin Hon Bala Mohammed Isah Gajere yace wannan ta'asar rashin imani ne da rashin mutunci dake daukar rayuwar mutane ba zai tafi hakanan ba.  
 
Hon Bala Mohammed Isah Gajere ya kaddamar da rabon tallafin da gwamnan jihar kebbi ya bayar dashi ga iyalan yan Sa'kai wadanda hare-haren'yan ta'adda ya shafa a garin Zuru.
 
Bagudu ya nuna alhininsa bisa mummunan harin da yan ta'addan suka kai a yankin Zuru ya jajantawa iyalan wadanda abun ya shafa tare da ba iyalansu tallafin Kudade, tare da alkawarin taimaka musu.
 
Gajere ya kara da cewa gwamnatin jihar kebbi ta ga ya dace ta aiko da wata tawaga mai karfi domin jajantawa iyalan marigayar tare da basu tabbacin cewa gwamnati ta nanan tana iyakar kokarinta wajen ganin ta kare mutuncin al'umma.
 
A cewarsa kowane daga cikin dangin mamacin za su karbi Naira dubu 200: yayin da za a baiwa iyalan wadanda suka samu rauni a yayin lamarin Naira miliyan biyu.
 
A ranar Lahadi da ta gabata ne gwamnatin jihar kebbi ta bada gudunmuwar kudaden ga iyalan yan Sa'kan da yan bindiga suka kashe a makon da ya gabata. 
 
Bala Gajere ya ce gwamnatin jihar ta kuma jajantawa masarautar Zuru tare da yin addu'ar Allah ya jikan wadanda suka mutu.