'Yan Bindiga Sun Sace Mutum 13 a Jihar Zamfara 

'Yan Bindiga Sun Sace Mutum 13 a Jihar Zamfara 

'Yan bindiga sun halaka mutum uku da sace wasu mutum 13 a wani hari da suka kai a ƙauyen Mayanchi cikin ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara. Harin da ƴan bindigan suka kai a ranar Litinin a ƙauyen na zuwa ne ƴan kwanaki bayan an sace mata 23 da wasu ma'aikata a ƙananan hukumomin Maradun da Talata Mafara. 

Wani mazaunin ƙauyen mai suna Aminu Mayanchi, ya gayawa jaridar Daily Trust cewa ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi. 
Aminu ya bayyana cewa daga baya ƴan bindigan sun je gidan wani marigayi Ibrahim Mayanchi wanda ya taɓa rike ma'ajin ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ) a Zamfara, inda suka yi awon gaba da ƴaƴansa gudu uku.
"Sun harbe mutum ɗaya bayan ya ƙi yarda su tafi da shi. Daga baya sai suka shiga wani masallaci inda wasu mutane ciki har da shugaban ƴan sakai na ƙauyen suka ɓoye, sannan suka tasa ƙeyarsu." A cewarsa. 
Daga cikin waɗanda ƴan bindigan suka halaka har da tsohon shugaban jam'iyyar APC na mazaɓar Mayanchi, Dahiru Maizabura, rahoton Premium Times ya tabbatar. 
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ba, ASP Yazid Abubakar, saboda layukan wayarsa a kashe su ke. Matsalar ƴan bindiga ta daɗe tana ci wa al'ummar jihar Zamfara tuwo a ƙwarya, inda rayukan mutane da dama suka salwanta da rasa matsugunansu da dukiyoyinsu.