Cire Tallafin Mai Ya Sa Masu Gidajen Mai Sun Fara Sayar Da Gidajen

Cire Tallafin Mai Ya Sa Masu Gidajen Mai Sun Fara Sayar Da Gidajen

Masu Gidajen Mai Sun fara sayar da Gidajen Man su kan matsin da suke fama da shi sakamakon cire Tallafin Mai da gwamnatin Nijeriya ta yi.

Kungiyar dillalan Mai ta kasa IPMAN ta bakin shugabanta ya sanar da cewa a Ibadan kawai akwai sama da mutum 40 da suka Sanya Gidajen Man su a kasuwa, akwai da yawa a wasu bangarorin kasa saboda rashin kyakkyawan yanayi a kasuwancin.

Shugaban ya ce mambobinsa dake sayar da tirelar man a kwana uku yanzu sai ya yi wata ba a sayar ba.

Ya ce motar Mai daya tana iya kamawa naira  miliyan 25 dakyar za ka samu naira dubu  500 riba 

Ribar ba ta iya isarka ka biya Ma'aikata ka yi wasu bukatu kamar na biyan haraji da sauransu.