Kotu ta baiwa DSS damar ci gaba da tsare Mamu har tsawon kwanaki 60

Kotu ta baiwa DSS damar ci gaba da tsare Mamu har tsawon kwanaki 60

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a yau Talata ta baiwa Hukumar Ƴan Sandan Farin Kaya, DSS damar su cigaba da riƙe Tukur Mamu, mai sasanta wa tsakanin ƴan ta’adda da iyalan wadandaa akai garkuwa dasu a jirgin kasan Abuja-Kaduna, har tsawon kwanaki 60.

Mai Shari'a Nkeonye Maha ya bada umarnin ne biyo bayan lauyan hukumar tsaro ta farinkaya ya nemi da a kara musu lokaci don cigaba da binkice akan Tukur.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa ‘yan sandan Masar sun kama Tukur  Mamu tare da iyalansa a ranar 6 ga watan Satumba, ya yin da yake kan hanyar sa ta zuwa Saudiyya domin yin Umara, daga karshe suka dawo dasu gida Najeriya.

A ranar Lahadin ta gaba ta jami’an na hukumar ta DSS suka jawa ‘yan Najeiya kunne kan tufar albarkacin bakin su akan kama Tukur Mamu.