Sarkin Musulmi bai mutu ba----Fadar Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi bai mutu ba----Fadar Sarkin Musulmi

 

Fadar Sarkin Musulmai a Najeriya ta yi magana kan jita-jitar rasuwar Sarkin Musulmi da ake yaɗawa. 


Fadar ta yi Allah wadai da jita-jitar da musanta labarin inda ta ce Mai Martaba, Sa'ad Abubakar yana cikin koshin lafiya.
 
Jami'in hulda da jama'a masarautar Aminu Haliru ne ya fitar da bayani  ya ce Masarautar Sarkin musulmi ta yi watsi da maganar, duk da dai kowa yasan dukkan mutum zai mutu idan lokacin barin Duniya ya zo.
Tun farko, shugaba kungiyar MPAC, Disu Kamor ya yi farali da labarin da ake ta yaɗawa kan rasuwar Mai Martaba. 
 
Kamor ya ce lafiyar Sarkin Musulmi garau babu abin da yake damunsa a halin yanzu. Kungiyar ta gargadi al'umma da su guji yada jita-jita da kuma tantance labarin kafin fara yaɗawa. 
 
Ta ce irin wadannan labarai marasa kan gado babu abin da za su kara illa rarrabuwar kawuna da kawo rudani. 
 
Sa'in Kilgori  Dakta Muhammadu Jabbi Kilgori shi ya tabbatar Sarkin Musulmi na raye "Ba mu san menene suke son cimmawa da wannan jita-jitar ba, amma tabbas Sarkin Musulmi yana cikin koshin lafiya." 
 
"Dazu ma muka bar jihar Kaduna domin halartar wani taro a birnin Tarayya Abuja kamar yadda ya saba."