Kwamitin Tsaro A Zamfara Ya Cafke Mutune Hudu Da Ake Zargin Saye Da Sayar Da Lambobin Mashin Na Jabu
Ya kara da cewa, “Wadannan dillalan da ke kan lambobin farantin babur na bugi da bayanai sun kasance suna sayar wa ‘yan bindiga lambobin farantin babur saboda munanan ayyukansu. A cewar shugaban, dukkan wadanda ake zargin za a mika su ga hukumar binciken manyan laifuka ta yansandan jihar domin ci gaba da yi musu tambayoyi. Da yake amsa tambayoyin manema labarai, dillalan lambobin babur din na bugi ya ce yana sayar da lambobi da takardu tsakanin N1500 zuwa N2500 kowanne.
Daga Aminu Abdullahi Gusau.
A ciga gada da kokarin da kwamitin da gwamnan Zamfara Bello Muhammed Matawalle ya kaddamar domin kulawa da harkokin tsaro, karkashin jagoran cin Abubakar Muhammed Dauran yayi nasarar cafke wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a kan jabun lambobin babur da kuma takardun su na bugi.
Da yake yiwa manema labarai jawabi a gidan gwamnatin jihar dake Gusau babban birnin jihar, shugaban kwamitin Hon. Abubakar Mohammed Dauran ya ce an kama wadanda ake zargin ne bisa bayanan sirri da suka samu.
Ya bayyana sunan dillalin da Ibrahim Rututu, inda ya ce shi Ibarahim yana saye da sayarwar lambobin babur na bugi da takardun bugi.
A cewarsa, a yayin da ake yi masa tambayoyi, dillalin ya amsa cewa ya rika sayen lambobin bugin ne da takardun su daga jihar Kaduna.
Da yake karin haske, shugaban ya ce an kama wasu da ake zargi da sayan wasu lambobin babur da bayanan bugi, inda ya ce wadanda ake zargin sun jagoranci rundunar ta Taskforce zuwa wajen dillalin inda aka kama shi.
Ya kara da cewa, “Wadannan dillalan da ke kan lambobin farantin babur na bugi da bayanai sun kasance suna sayar wa ‘yan bindiga lambobin farantin babur saboda munanan ayyukansu.
A cewar shugaban, dukkan wadanda ake zargin za a mika su ga hukumar binciken manyan laifuka ta yansandan jihar domin ci gaba da yi musu tambayoyi.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, dillalan lambobin babur din na bugi ya ce yana sayar da lambobi da takardu tsakanin N1500 zuwa N2500 kowanne.
A wani labarin kuma, Hukumar Taskforce ta kama wani Uzairi Isah da babur Boxer da cikakken tankin mai da ake zargin na ‘yan bindiga ne da ke aiki a jihar.
“Mun kama shi ne saboda muna zargin shi dan fashi ne amma bincike zai zurfafa don gano gaskiyar shi”.
A cewar shugaban kwamitin, Hon. Abubakar Mohammed Dauran, lokacin da ake masa tambayoyi ya yi ikirarin cewa shi direban babur ne da ke aikin Okada a Abuja.
managarciya