Kamfanin Boska Ya Duba Lafiyar Idanun Mutane Kyauta a Gombe Daga Habu Rabeel  Gombe

Kamfanin Boska Ya Duba Lafiyar Idanun Mutane Kyauta a Gombe Daga Habu Rabeel  Gombe

 

A yau laraba ne Kamfanin Dexa Medica dake  sarrafa maganin nan na Boska ya ware rana ta musamman ya duba lafiyar Idanun al'umma kyauta a garin Billiri a jihar Gombe.

 
Jagororin Kamfanin na Dexa suka ce sun ware wannan rana ce musamman domin ilmantar da jama'a muhimmancin lafiyar su ta hanyar amfanin da magungunan kamfanin Boska wajen rage radadin ciwon dake damun su  a kowacce rana.
 
Da yake jawabi a wajen taron a garin na Billiri kan dalilin ware wannan rana dan duba lafiyar idanu kyuata babban Sakataren kamfanin na Dexa Medica mai kula da yankin arewacin Najeriya Mista Ayodele Opowoye cewa ya yi suna so suji daga kwastomomin su ne da suke amfanin da magungunan su su kuma ga ta yadda za su taimaka musu a jihohi 7 na  fadin tarayyar kasar nan a cikin watan nan na Yuni 2022.
 
Daruruwan Yan kasuwa ne da mabukata gami da mazauna garin na Billiri suka dinga tururuwa dan zuwa su ga likitocin da suka zo dan duba lafiyar su da ya shafi idanu kuma a basu tabarau da magunguna kyauta.
 
A cewar sa burin Kamfanin shi ne yaci gaba da samar da ingantaccen magani ga kwastomomin sa da kuma daukacin al'umma baki daya.
 
Wani daga cikin masu amfani da maganin na Boska da yaci moriyar aikin Ido mai suna Joseph Isaac, rokon kamfanin ya yi da cewa yana fata wannan shiri nasu zai dore domin taimakon al'umma musamman marasa galihu.
 
Sannan sai ya godewa kamfanin bisa wannan kokari na su na duba lafiyar idanu da bada tabarau gami da magunguna kyauta a wannan rana da suka ware ta musamman ta ranar Boska Day campaign free for health care services.