"Crocodile tears"  2027 Talaka APC Zai Zaba Domin Biyan Bukatar Uwayen Gidansa 

'Yan  Najeriya sun san halin da suka tsintsi kansu bayan da BUHARI ya kifar da gwamnatin Alhaji Shehu Shagari a shekarar 1983. Lokacin shinkafar da gwamnatin Shagari ta sawo ta sauke farashi, 'yan Niajeria cewa suke wari keda ita, ba su so. Da BUHARI ya karbi mulki, sai ga su suna bin layi soja da bulala yana dukar su , da kyar za’a sayar ma da mudu uku na shinkafa,  suga da gisihiri,  madara suka zama gold, Burodi farashinsa ya tashi duk mai shekaru irina, ba bako ba ne ga abinda na fada.  Duk da sanin haka, 'yan Najeriya suka wanke Buhari tas! Suka taimaka BUHARI ya kifar da gwamnatin Jonathan ta hayan zabe a shekarar 2015. 

"Crocodile tears"  2027 Talaka APC Zai Zaba Domin Biyan Bukatar Uwayen Gidansa 
 
"Crocodile tears" is an idiom that describes a fake or insincere display of emotion, such as someone who pretends to be sad or sorry when they are not
 
"Crocodile tears"  hawaye ne  da ke nuna nadama ko bakin ciki amma a hakikani , hawayen karya ne. 
 
'Yan  Najeriya sun san halin da suka tsintsi kansu bayan da BUHARI ya kifar da gwamnatin Alhaji Shehu Shagari a shekarar 1983. Lokacin shinkafar da gwamnatin Shagari ta sawo ta sauke farashi, 'yan Niajeria cewa suke wari keda ita, ba su so. Da BUHARI ya karbi mulki, sai ga su suna bin layi soja da bulala yana dukar su , da kyar za’a sayar ma da mudu uku na shinkafa,  suga da gisihiri,  madara suka zama gold, Burodi farashinsa ya tashi duk mai shekaru irina, ba bako ba ne ga abinda na fada.  Duk da sanin haka, 'yan Najeriya suka wanke Buhari tas! Suka taimaka BUHARI ya kifar da gwamnatin Jonathan ta hayan zabe a shekarar 2015. 
 
Tun shakarar BUHARI ta farko a matsayin zababben shugaban kasa, mutane suka fara gano akwai gyara. Haka suka yi ta bashi uzuri har ya shekara hudu. Dan Najeriya bai daddara ba a 2019 ya sake zaben BUHARI saboda kada jama’iyar BUHARI ta APC ta fadi , BUHARI ya ji kunya. Suka bi duk hanyar da suka bi, BUHARI ya kada Atiku Abubakar da jama’iyarsa ta PDP. BUHARI ya ganawa talaka azaba da tsanani na tsadar rayuwa, rashin aiki da rashin abin hannu. Ya rufe boda, ya Kara kudin mai, ya cire tallafin Gas  da kalanzir, ya canza kudi ya cire tallfin Hajji, ya gagari yaki da 'yan amsar kudin fansa da suka samu gindin zama a lokacinsa. 
 
A haka , BUHARI ya fito 2023 ya ce talaka ya zabi jam’iyarsa ta APC domin dan takarar jama’iyar watau Bola Ahmed Tinubu, zai dora daga inda BUHARI ya tsaya kuma aka zabe shi. Bayan zaben Tinubu, an jiyo BUHARI na cewa ‘ “na ji dadi da Tinubu ya Kara kudin mai"  ma’ana, yana bin qudirinsa na ganin talaka ya ci gaba da zama cikin halin “ ha’ula’i.  Yau !  “ The rich also cry  bala’in ya game kowa da mai shi da marashi. Kowa kuka ya ke amma!  Wallahi "Crocodile tears"  ne, hawaye ne  da ke nuna nadama ko bakin ciki amma a hakikani , hawayen karya ne. 
 
Na rantse da Wanda rayuwata take a hannunsa, akwai miliyoyin 'yan Najeriya da za su sake jefawa Tinubu kuri’a idan Allah ya Kai mu zaben 2027 domin hujjar su , APC jama’iyar Buhari ce da uwayen gidansu, su kuma da uwayen gidan su; şu fadi zabe, gara şu dawwama a halin kuncin rayuwa da suke ciki. Uwayen gidan su saka a bakinsu, su kuma ba su iya korewa bakinsu kuda. 
Haka abin yake a tarayya da jihohi. 
 
Sadiq Abba Abubakar Jr.