'Yan Bindiga Sun Kashe Mata Biyar Bayan Sun Dawo Gona a Sakkwato

'Yan Bindiga Sun Kashe Mata Biyar Bayan Sun Dawo Gona a Sakkwato

 

'Yan bindiga da ake zargin yaran sanannen dan bindigar nan ne Bello Turji sun kashe mace biyar yayin da sama da 10 ke a asibiti a Sakkwato.

 
Matan da ake zaton sun kai 18 a cikin doguwar motar Bus suna  zaune a kauyukkan Lugu da  Danzange da  Modaci a karamar hukumar Isa a jihar Sakkwato sun tafi gona ne a karamar hukumar Kaura ta jihar Zamfara, kan hanyar su ta dawowa ne suka hadu da maharan suka buda masu wuta.
tify;">Majiyar da ta shaidawa manema labarai  cewa matan sun tafi gona ne domin cire amfanin gona a yankin Ƙaura suna saman hanyar dawowa ne maharan suka buda masu wuta anan take cikin motar mace biyar suka rasu, aka harbi direban mota Abubakar Modaci a kafa an kai shi asibitin Shinkafi da Zurmi tare da sauran matan da ke cikin motar da suka samu a rauni a harbin.
Harin da ya faru a Laraba da marece ya yi sanadin jikkata matan da ba su ji ba su gani ba, abin da wasu ke danganta ramuwar gayya ce 'yan bindigar ke yi saboda harin da sojoji suka kaiwa shugabansu a yankin.
Shugaban karamar hukumar Isa Honarabul Abubakar Yusuf Dan Ali ya tabbatar da harin kuma ya ce karamar hukunarsa tana kan kokarinta kan wadanda suka jikata.
Ya ce abu ne da Allah ya kawo matan mutanen karamar hukumar Isa ne sun tafi gona ne don su yi aiki wannan lamarin ya rutsa da su, wadanda ke raye ana kokarin kula da su a asibiti, Allah ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

A wata mai kama da wannan 'yan bindigar sun kashe mutum biyu a yankin Jabo dake cikin karamar hukumar Tambuwal a ranar Talata data gabata.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jiha DSP Sanusi Abubakar wakilinmu ya kira shi a waya ya kuma tura masa sako, amma har zuwa hada rahoton bai ce komai kan harin da 'yan bindiga ke kai a sassan jihar Sakkwato ba.