LISSAFIN ƘADDARA: Fita Ta 15 & 16
da sallama Alhaji kamalu ya shiga gidansa ba kowa a tsakar gida sakamokon dare yayi sosai,a ɗan madaidaici falon gidan ya samu matar gidan tanata safa da marwa,ko kallonta baiyiba ya kama hanyar dakin shi kai tsaye sai dai amon muryarta ya dakatar dashi "kai dai wallahi wallahi Kamalu kaji kunya wato tunda ka fara zance zaka dawo da waccan annamimiyar matar taka da Allah bai bata kwan ɗa namiji ba shikenan muka zama banza ni da ƴaƴana,ni banga abunda aurenta ka kareka ba banda asara da tozarci"ta ƙarasa faɗa tana jirjiza ƙirji da ƙugu wani kallon banza Abban Ameenatuh
LISSAFIN ƘADDARA:
*ZAINAB SULAIMAN*
(Autar Baba)
Not edited
*DEDICATED TO SHAMSIYYA USMAN MANGA*
Marubuciyar Kalubalen rayuwa
P15& 16
Shewa mazan gurin duka suka saka yayin da Abban Ameenatuh da amininsa Alhaji Sabo suka kai hannu suka kashe kamar wasu ƴan daudu,sai da suka gama dariyar shaƙiyancinsu sannan alhaji Sabo yace"ina yinka mutumina wallahi kai kama fini mugunta yanzu nawa kake gani zan bayar sadaki da kudin lefe,dan gaskiya bazan iya haɗa kayan lefe ba"sai da Abban Ameenatuh ya gyara zama kafun yace"ka bada 1m ai yayi ko"ya fada yana kallon sauran abokansu na wajen da son jin abun da zasu ce "haba dai Kamalu hauka ake akan wannan ƴar tayin yarinyar na bada milyan ɗaya sai kace wacce zan auri cikakkiyar budurwa"da mamaki Abban Ameenatuh yace"ai kai ne ma babbar shedar ƴata cikakkiyar budurwace duk ba wani abu ya shiga tsakaninku ba,amma banason ja ka bada budu dari takwas in yayi maka to in baiyi maka ba kum Umma ta gaida aysha"shiru sukayi gaba ɗaya na ɗan lokaci kafun Alhaji Sabo ya janyo jakar da ke kan teburin gabanshi ya ciro kuɗi ya miƙawa alhaji Kamalu yace"ga shinan na sanka da baƙin naci in kace abu kake so"wata kalar dariya basawa Kamalu ya saka kafun yace"haka akecewa,amma wannan kuɗin dama a account kasamu saboda kasan ina da masu halin ɓera a gidan nawa"mikewa Alhaji Sabo yayi yana cewa "in kaga dama ka ɗauka dan bazan iya tura maka kudi ba gaskiya kan gani ɗazu naje banki na cirosu,dan Allah ku fitar mun a ofishi zan rufe"tashi sukayi gaba ɗaya sukayi musu Allah sanya alkairi kowa ya kama gabanshi,
da sallama Alhaji kamalu ya shiga gidansa ba kowa a tsakar gida sakamokon dare yayi sosai,a ɗan madaidaici falon gidan ya samu matar gidan tanata safa da marwa,ko kallonta baiyiba ya kama hanyar dakin shi kai tsaye sai dai amon muryarta ya dakatar dashi "kai dai wallahi wallahi Kamalu kaji kunya wato tunda ka fara zance zaka dawo da waccan annamimiyar matar taka da Allah bai bata kwan ɗa namiji ba shikenan muka zama banza ni da ƴaƴana,ni banga abunda aurenta ka kareka ba banda asara da tozarci"ta ƙarasa faɗa tana jirjiza ƙirji da ƙugu wani kallon banza Abban Ameenatuh ke binta da shi har ta kai aya sannan ya mata kallon sama da ƙasa yace"gara ita iya ƴaƴa mata kawai ta haifa sannan waya ma ya sa ni tunda ta jima bata haihuba yanzu inta tashi haihuwar ta haifi namijin keda ,kika haifamun ɓeraye fa,sannan da kikecewa asara da tozarci ta jamun a gidan ubanwa na taɓa faɗa miki haka,ke da nayi ta tabbaka asara tunda aureki har yau ban daina ba ga dai ƴaƴa maza kin haifa amma ɓeraye,sannan yau wata guda kenan dayi gobara a company na shin wannan ba asara bace ko lokacin ina tare da maryam nayita,sannan wata uku baya company leda ta da yake dawakin dakata shima ya kone,ki kiyaye ni wallahi kafun nayimiki walmakalafatu,bani guri na wuce daƙiƙiya kawai"ya fada yana bangajeta yayi gaba abunsa ya barta da ƙunar zuciya,
4:50am ya farka a bacci ya nufi ma'ajiyar kuɗinsa dan yasan indai a gidan wani mahaluƙi ya ga ni to ya zama ba rabonshi ba,gida biyu ya raba kuɗin ɗaya yasa a ƙasan katifa ɗaya yasa a cikin litattafansa saboda bai taɓa a jiya a gurin ba,yale kuwa sama ko ƙasa ya nemi kuɗi sukace ɗaukemu inda ka ajemu,tashin hankali wanda ba'a sa masa rana kenan ya gama bajet ɗin kuɗinsa akan gyaran company ledarsa sai kuma sama ta ka wani yazo ya rusa masa bajet!"bazai yiyu ba!!" ya faɗa da ƙarfi yana ƙara hargitsa ɗakin ya koma kamar na mahaukata,a haukace yayi ɗakin babban yaronshi da bai haura 13 to 14 years ba,bai ƙara firgita da lamarin ba dai da yaga yaron baya nan,kai tsaye ɗakin matarsa ya nufa yana bambami,daƙyar take iya motsa idanta saboda tsabar baccin da ke cinta "an yanka ta tashi ina ɗan ki!!?"ko kallon banza baisamu arziƙin ayimishi ba balle na arziƙi ta ja! tsaki ta juya kwanciyarta ta kara bararrajewa a gado,duka ya kai mata sosai yana kara maimaita "ina ɗanki"cikin hargagi yake magana wanda hakan ya haddasa mata tsoronshi a fili cike da in ina tace "yayi tafiya yau kwana uku kenan yace sun tafi lagos"kallon hadarin kaji ya bita da shi kan ya samu yace"to kenan ke ko karamin yaronki wani a ɗauke kuɗin auren waccan ƴar?ke! kalle ni nafiki fitsara da shiga bariki wallahi ko ki futomun da kuɗina ko nayi miki lahani kowama ya huta"ya karasa maganar cike da tsageranci.,
AUTAR BABA CE
managarciya