√√√√√ MEE'AD fan's kuyi hakuri da rashin post akan time, saboda wasu dalilai. √√√√√√
27 ~ 28
Bayan sun kammala lunch baki dayansu a falo suka yada zango, sai hiran yaushe gamo suke tare da Majeed, haka suka kasance har lokacin sallah yayi anan kowa ya nufi bed dinsa yayinda su kuma mazan suka nufi masallaci.
" Bayan sun idar da sallah isha gida suka shigo baki dayansu dan yin hirar yaushe gamo a karo na biyu kafin suje ga darning saida suka sha hirarsu mai dadi sosai.
Amal na hango zaune kusa da Mee'ad sai murmusawa take, fuskarta cike da farin ciki ta dago fiska ta kalli Mee'ad din kafin tace Bloody ashe kin fini gaskiya dama haka Yaya Majeed ya hadu sosai babban gaye bashida makusa kota ina gaskiya, ihm! Ya burgeni har cikin zuciyata dalilin da yasa naji kamar zuciyar tawa ta fara kamuwa da kaunarsa marar adadi,"
Mee'ad ta dubi Yayartata hade da jan dogon numfashi gami da daura hannunta daya bisa kafadarta ta kuma kirkiro murmushi kafin tace ki kwantar da hankalinki sisina idan kina son Yaya Majeed ne kar kiji komai nima zan zamo mai mara miki baya kinga sai muyi yakin tare ko ?"
Amal tace sosai ma! naji dadi da kikai saurin fahimtata na kuma gode sosai, murmushi Mee'ad ta kuma yi kafin tace bari naje kitchen na dama tea kinji sistona, Amal tace to sarkin tea saikin dawo, bata tsaya cewa komai ba ta nufi kofar dazai sadata da kitchen din.
" Bayan sun kammala cin abincin dare, kowa part dinshi ya nufa dan shirin kwanciya, domin mutan gidan da wuri suke kwanciya,"
Amal ce zaune bisa kan gado tana faman chat da wayarta, Yaya Majeed ne yayi knocking kofar dakin ta ce waye ? Baiyi maganaba ya tura kofar ya kutsa kai cikin kawai, zaune ya sameta jikinta sanye da wata doguwar sleep mara nauyi shiga yayi da sallama kafin ya sami kujeran dake gefen gadon ya zauna ya zuba mata ido,"
" Yakai 15min da zama baice komai ba, itama shiru tayi batace komai din ba, yajaa dogon numfashi cike da kulawa ya dubeta kafin yace kanwata farin cikina kuma abar alfaharina dftn kin wuni cikin koshin lfy ? A yangace ta dagokai tana yamutsa fuska kafin tace lfy alhmdlh, ya gajiyar hanya kuma ? Murmushi yayi kafin yace alhmdlh,"
"Itama murmushin tayi kafin ta haye kan gado sosai ta fara gyara blanket tana shirin kwanciya Majeed ya mike tsaye yana fadin ah kwanciya zakiyi kenan ?
"Shiru tayi bata bashi amsa ba jin shirin da tayine ya sanyashi ce mata mukwana lfy ko ?"
"Tayi kasa da murya kafin tace gud night kawai ta kwanta ta lullube jikinta, ganin hakan da tayine ya sanyashi fita daga bed din nata tinani faal zuciyarsa".
%%%%%%%%
" Yana barin dakin Amal kai tsaye corridor dazai sadashi da part dinsa ya nufa, tafiya yake yana tinane2 har ya kawo bakin wani kofar daki juyawan da zaiyi ya hango Mee'ad zaune bisa karamar kujera hannunta rike da system sai danne2 take a cikin dakin murmushi yayi kafin ya shiga dakin kasancewar kofar dakin a bude take ya shiga da sallama,"
Amsa masa sallaman tayi fuskarta dauke da murmushin jin dadi, kujerar dake gefenta ya jawo zama yayi yana cewa Babbar Kawata ya kk ? Har yanzu baki daina son computer taba abinki, murmushi Mee'ad tayi kafin tace haba Yaya ai mai hali baya taba daina halinsa ko ba hakaba ? Jijjiga kai yayi kafin ya kyalkyale da dariya, a dakile ta kalle shi kafin tace au daria ma na baka kenan ?
"Majeed ya kara gyara zama ya kunshe dariar tasa Yana cewa kedai har yanzu wayon da kike dashi baki daina ba, shiru tayi bata tanka ba, yaci gaba da cewa toya school din dai ? Ana kokari ko ? Ahh na manta ashe ke guruwa ce tin kafin nabar kasar nan, murmushi Mee'ad tayi amma bata tanka masa 'a karona 2,"
Majeed ya dawo da nutsuwar shi baki daya kafin ya dubi Mee'ad cikin ido yace kanwata miyasa baki taba turamin wasika ba koda sau dayane tin lokacin dana tafi ?"
"Murmushi Mee'ad tayi kafin tace hmm! Yaya kenan ta iya yiyuwa ma na tura maka text din kace Bloody ce ta tura maka, murmushi yayi kawai kafin ya nunata da yatsa cikin tsokana yace kinga Bloodynki tafi kaunata kenan fiye dake! Murmushi Mee'ad din tayi tana cewa kayi hakuri Yaya gaba daya bana samun lokacine shiyasa ban tura maka wata wasika ba amma na tuba bazan kara ba, ta kama kunnenta ta durkusa kasa tana cewa sorry our bro I apologise to you!
"Murmushi yayi kafin ya durkusa ya cire hannun data dora akan kunnenta yana cewa my best friend I accept ur apology kinji ? Jinjina kai tayi tana murmushi shima murmushin yayi ya kuma kamo hanunta ya zaunar da ita bisa kujerar data tashi,"
Kura mata ido yayi yana murmushi kafin yace kanwata kinsan girman soyayyar da nakema bloodynki kuma ?
"Jijjiga kai Mee'ad tayi kafin tace na san hakan tinda gashi ya bayyana a cikin kwayar idonka, gyara zama yayi yana mai cewa nasan duk Wanda ya kalli cikin idona idan har yasan abinda yakeyi tozai iya gano irin matsananciyar soyayyar da nake mata, yajaa dogon numfashi muryarsa cike da damuwa kafin yace kinsan mi yake faruwa kuwa ?
Yanzu haka daga bed dinta na fito na kuma kalli canji sosai a tare da ita komi ya jawo hakan ohoo! Ya danyi shiru kafin yaci gaba da cewa a matsayinki na Babbar Kawata wani irin taimako zaki bani wajen shawo kan yar uwarki ?"
Dogon numfashi Mee'ad taja kafin tace ni nasan sistona Amal tana matukar kaunar ka, kawai inaga kayi mata wani abu ko kuma yanayine ya hanata buda maka hakan, ta gyara zama kafin taci gaba da cewa ka shirya mana fita shan ice cream gobe inada tabbacin a wannan wajen zaku shirya coz I know her well".
Murmushin jin dadi Majeed yayi kafin yace insha Allahu zanyi iya bakin kokarina naga fitarmu gobe ya kasance".
Daria Mee'ad tayi kafin tace Ina yinka sosai Yaya Majeed domin koba komai kai gwarzon namijine wanda zai iya sadaukar da baki daya farin cikinsa dan wacce yake muradi.
Shima daria yayi kawai ya kuma bita da kallo yan yabon hankali da wayon Mee'ad din a cikin zuciyarsa.
Nan sukaci gaba da fira har 9;30 kafin yayi mata sallama ya fita, binsa da kallo Mee'ad tayi tana mai cewa mukwana lfy farin cikina, tabbas zuciyata cike take da dumbin soyayyar ka mara misaltuwa 'amma na gwammaci na sadaukar da soyayyar da nake maka ga yar 'uwata sbd naga zuciya, ruhi da baki dayan soyayyar ka ka mallaka mata ta share hawayen daya biyo kuncinta tana mai furta kalmar " WALLAHU GALIBUN ALA AMRIHI ".
Murmushi tayi kafin ta dauko system dinta taci gabada dannawa zuciyarta cike da matukar damuwa, ta kasa ci gaba da assignment din da takeyi, ajiye system din tayi ta nufi toilet danyin alwala.
Majeed kuma bayan ya koma dakinsa wanka ya dauro alwala sai da yayi shafa'i da wutiri, yayi addu'a sosai kafin ya kwanta bisa kan katafaren gadon dake shimfide a dakin nasa, ya dade yana tinanin Amal da 'abinda Mee'ad tace masa kafin bacci barawo yayi awon gaba dashi.
Washe gari misalin karfe 9 dai2 Majeed ya gama shiryawa tsaf cikin shigen daya saba na kananun kaya yayi kyau sosai sai kamshin tirare yake zubawa, ya shigo falo Umma da Mommy ya samu zaune suna hira, sunkuyawa yayi ya gaishesu kafin yace Mommy ina twins ?
"Murmushi tayi kafin tace sunbi Hajiya tin jiya kasan anyi musu hutu, yace yauwa ina sauran suke ya karasa maganar yana sosai kai, Umma ce ta ce suna sama, bata karasa rufe baki ba ya nufi steps din da zai sadashi da dakin nasu," Binsa da kallo sukayi suna murmushi.
Kai tsaye dakin Mee'ad ya nufa fuskarsa faal farin ciki, ya tura kofar ya shiga hangota yayi a bakin dress mirror tana daura kallabi, karasawa kusa da ita yayi kafin yace kai kinga yadda kikayi kyau kuwa Kawata?
" Murmushi Mee'ad tayi kafin tace tnx Yaya, ta karasa daura kallabin ta juyo fuskarta dauke da murmushi take fadin ya kaganni na fito kuwa ?
Daga yatsu biyu na hanunsa yayi yana nuna mata alamar tayi kyau, tnx tace kafin tace masa Yaya Majeed ka zauna mana yace no ba zama zanyi ba nazo na duba yaya Kawata ta tashi ne tace da gaske ? Yace ga 'alama kuma, daria tayi tana mai binsa da kallo.
Ya matsa kusa da ita kafin ya mika mata hannu yana fadin kinga ban tabayin kawa mace ba sai a kanki kuma gashi nayi sa'an yin kawa mai hangen nesa zaki iya kulla kawance na har abada dani ? Murmushi Mee'ad tayi kafin tace sosai ma, yace to idan zaki iya hakan bani hannunki mu kulla 'alkawari mika hannunta tayi da nufin su gaisa,"
Keee taji an fada daga bakin kofa a tsorace suka kalli bakin kofar wa zasu gani Amal ce tsaye ta rike kugu sai haki take...............
Mai karatu biyoni kasha labari
Pls vote, comments and share Fisabilillah.