MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 44 Zuwa 45
Page 44---45
Nasir na kwance cikin ɗakinsa yana tunanin Bilkisu, yayi mamaki sosai yanda ta wani share da lamarin abin da ta aikata a gun saukarta, amma kuma sai ya samu kansa da jin shima bai kyauta ba, ya yi fushi yabar gun batare da an watse daga walimar ba, ƙanwarsa ta gaya masa Bilkisu bata ji daɗin hakan ba, to ya zai yi ?
Ji yayi kamar ana taɓa masa ƙafa, dan haka ya kai hannu ya shafa ƙafar, sai dai bai ji komi ba, dan haka yaci gaba da tunanin ya kamata yaje gidansu Ibnah yanzu bama sai anjima ba, tunda safiya ce yanzu, idan yace sai dare haƙiƙa ba zai iya jurewa ba.
Ji yayi an sake ja masa yatsan ƙafarsa da ɗan ƙarfi, dan haka ya buɗe idonsa ya kalli ƙafar, amma ba komi gun cikin ikon Allah.
Rufe idonsa ya sake yi yana taɓe bakinsa alamar koma miye shi ya sani dai.
Sai dai wani uban zafi da ya ziyarci kwanyar kansa yasa shi tashi zaune ba shiri ya riƙe yatsan da ke masa ciwo kamar kunama ta halbesa.
Kamar ance kalli ƙasa, sai ya ga wani ƙaton yatsa sai motsi yake ba tare da komi ba.
Idanuwa ya zaro waje yana tunanin daga ina wannan yatsan yake ?
Ya akai babu jini ko ɗigo a jikin yatsan ?
Gama tunanin hakan kenan yaga yatsan na matsawa kamar yanda ƙafa ke tafiya, ya nufi ƙofar ɗakin.
Shi dai sai ya saki baki yana kallon( ikon Allah, wai an rufe tsohuwa da ranta).
Abin kamar a Film yaga yatsan ya rufe ƙofar ɗakin garam!
Nan take sai wani mashahurin baƙi ya mamaye ɗakin wanda ko tafin hannunsa bai iya gani .
Cikin wata murya mai matuƙar ban tsoro ya ji ana ambatar sunansa ...
"Nasirrrrr !
Tamkar raɗa ake masa a kunne haka ya ji ana ambatar sunansa da wasu kalan muryoyi masu ban tsoro .
Jikinsa ya fara kyarma ganin yanda wasu manyan halittu ke gilmawa a cikin duhun ba kyan gani, kuma su kaɗai yake iya gani.
Cikin ƴar sauran jarumtarsa yace...
"Ko waye ya bayyana mana idan ba tsoro ba.
Miye amfanin wannan shirmen ?
Yana rufe baki ɗakin ya fara girgiza kamar zai kife baki ɗaya ya ji yana juyawa daga inda yake zaune.
Zuwa can ya ji wani irin kuka kamar na mace kamar na namiji ana ambatar sunansa.
Zuwa yanzu ya gama tsorata da lamarin dan haka ya fara ƙoƙarin kunna fitilar wayarsa.
Sai dai yana haskawa yaga fuskar wani ƙaton mutum bakinsa buɗe babu haƙora, amma sai jini ke zubowa mai wani irin ja, ga hancinsa da uban tsawo kamar an miƙe sanda tsaye , sai wasu ƙananan ƙwari ke shigewa ciki ba kyan gani.
Idanun kuwa sunyi jajir sai wani baƙin ruwa ke zubowa kamar an kunna fanfo.
Runtse ido yayi yana dan tunano addu'a amma ina ba addu'ar da ya tuna dan haka ya dage iyakar karfinsa ya kwartsa uban ihu.
Hakan yayi dai-dai da yayewar ɗakin ba Nasir ba alamarsa babu kan komi ya koma yanda yake sai wayarsa da ke yashe a ƙasa.
Sun luluƙa cikin sararin samaniya sai tsula gudu su ke ba ji ba gani, Aljana Rayhanatu tace, "Ya ke Gimbiya Raƙiyyatul Zayyanul murrash, ki sani cewa daga bakin dajin ban isa na ƙara taka kafata ba, haka kema haka ba za ki iya shiga cikin shi ba, domin irin tsarin da ke cikinsa jinin sarautar masarautar su Sarki Abduljalal bin Uwais ne kawai ke iya shiga cikin dajin ba tare da wani abu ya same shi ba."
Murmushi Raƙiyyatul Zayyanul murrash tayi tace,
"Shin ban gargaɗe ki akan yunƙurin kawo yaudara ko ha'inci a cikin tafiyarmu ba ?
To ki sani ina tare da kambum sihiri a hannuna wanda duk inda naso zan iya shiga na fita ba tare da wani hatsari ya tunkareni ba, dan haka da ni, da ke duk zamu tunkari dajin ba ko haifi sai mun shiga mun ɗauko Huraira."
Ita dai Bilkisu ban da tasbihi babu abin da take yi, ga gabanta dake tsananta faɗuwa, tana jin zuciyarta na ambatar sunan Nasir .
Haka suka shafe kwanaki tara basu haɗu da komi ba har suka isa dajin, wanda tun daga nesa suka fara jin wani yanayi mai kama da hunturun sanyi na ratsa su.
Suna sauka bakin dajin suka ga hanya guda ɗaya rak ce da zaka bi ka shiga cikin dajin.
Anan Aljana Rayhanatu ta fashe da kuka ta dubi Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash tace,
"Ki yi sani cewa dajin nan bai jin digiri duk wanda ya shiga cikinsa zai yi barci na tsawon shekaru goma ne cire bai farka ba, ko itama Huraira shi ne abin da take yi tun ranar da aka kaita cikinsa."
Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash ta dubi Bilkisu tace,
"Shin kin shirya zuwa ƙwato mahaifiyarki ?
Cikin ƙwarin gwiwa Bilkisu ta ɗaga kanta, domin ta kasa cewa ko da ƙala ba inba addu'ar da take yi ba dare da rana yau tsawon kwanaki tara kenan sallah da cin abinci kawai ke tsaida ta sai kuwa lalurar fitsari ko bayan gida.
Cikin daka tsawa Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash ta ba Rayhanatu umarnin ta wuce gaba su shige cikin dajin.
Dole Rayhanatu ta shige gaba suka bi bayanta, da ka ganta kasan a tsorace take.
Sai da su kai nisa suna kallon yanda dajin yake ba wani abin tashin hankali ko ban tsoro Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash tacm dubi Aljana Rayhanatu ta e, "Tur da ke munafukai , da kin ɗauka munafurcinki zai sa mu fasa shigowa ne ?
To ki sani kin riga kin makara domin.....
Kawai ji sukai tayi tsit bata ida abin da zata ce ba.
Aljana Rayhanatu ta taɓa ta, tace "Yanzu kin gane abin da nake nufi ko ? Lallai kinyi wauta gaske da kika kawo kanki cikin wannan dajin.
Ta bushe da dariya ta dubi Bilkisu tace, Gimbiya matar Sarki barka da zuwa masarautar ki gidan mijinki Shugaba Abduljalal bin Uwais."
Sai wasu kyawawan mata ɗauke da tiraruwa sun fito daga cikin wani gida da yanzu ta ganshi a gabanta ma ita.
Addu'a taci gaba da yi amma abin mamakin shi ne yanda baki ɗaya dajin ya ɗauki karatun Alƙur'ani cikin murya mai daɗin gaske.
Haka tana ji tana gani rabi matan suka shige cikin gidan suna watsa mata furanni mau ƙamshin gaske.
Suna shiga taga fadar sarauta mutane zaune anata harkokin Sarauta.
Sarkin na zaune kan kujera baka isa kaga fuskarsa ba duk nacinka, ita dai kamar raƙuma haka ta bisu har zuwa gaban Sarkin.
Sai alokacin ta fahimci karatun da take ji daga garesa ne ashe .
Wai ɗaki ya nuna sai taga an nufi ɗakin da ita kai tsaye.
Suna shiga ciki taga Inna Huraira kwance kamar gawa.
Da gudu ta isa gunta tana girgiza ta amma ko motsi batayi ba.
Zuwa can sai da Sarkin ta shigo fyksa cike da murmushi yace,
"Marhababuki da zuwa gidan mijink,i ki sani an ɗaura mana aure ga sadakinki, ya miƙa mata wasu mata masu kyau da tsadar gaske.
Kallo guda tayi masa ta fahimci shi ne take yawan mafarkin ya zama mijinta wata mace ta zo ta raba su .
Batasan ya akai ba ta samu kanta da amsar kayan.
Ji tayi ya kama hannunta ya saka mata wani zobe, suka bi ta wata ƙofar suka ɓulla wani ɗaki mai kyan gaske .
Ta rasa abin da yasa ta ke binsa, komi yayi da ido kawai take binsa da shi .
Jawo ta yayi jikinsa ya kama sunsunata yana jan wani irin nishi .
"Haƙiƙa ina sonki, ba zan bari na rasa jirgi ba Bilkisu."
Ita dai ta kasa cewa ƙala ta lafe jikinsa kawai tayi lub.
To fa ko dai Bilkisu ta afka cikin soyayyar Abduljalal bin Uwais ne ?
Dan jin gaskiyar bibiyi alƙalamin Haupha
managarciya