MEE'AD:Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta Ashirin Da Shida

MEE'AD:Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta Ashirin Da Shida
     
           ***CONTINUE***
55 ~ 56
Ƙura masa ido tayi hannunta dafe bisa kuncin ta Ma..jee..d nika mara ? Ta faɗa murya a sarƙaƙe! Kai ya ɗaga da da'alamar ya mareta ɗin yace dana mareki sai akace miki zaki iya ramawa ? Ya nunata da yatsa to bari kiji daga rana irinta yau ko kallon banza kika sake kika ƙarayimin  wallahi duka ne zai biyo baya don naga rainin hankalin naki ya fara yawa yana gama faɗin haka ya nufi kujera ya zauna fuskarsa cike da takaicin abinda Amal ɗin tayi.
Amal binsa da kallo tayi zuciyarta cike da ƙuna take faɗin a haka za'a ƙaƙabamin kai na aureka ? wallahi bazan ta'ba auren ka ba kaje can ka nemo wacce zata iya jure halayyarka, amma tabbas ni zuciyata akwai wanda takeso bakai ba tana gama faɗin haka ta nufi ƙofar fita daga falon harta fita sannan ta juyo tsayawa tayi ta kama ƙugu tace kai Majeed! bari kaji abunda nake 'boyewa ban faɗa maka ba wallahi na tsaneka, bana sonka, idan harka sake ka bari aka haɗa auren mu tozan kashe kaina na kuma kasheka saboda banga amfanin auren ba, ficewa tayi daga falon sannan ta buga ƙofar da ƙarfin gaske.
"Bin ƙofar yayi da kallo yana jijjiga kai Allah ya shiryar dake yasa ki gane abunda kk aikatawa ba mai kyau bane," tashi yayi ya nufi ɗaki jakar system ɗinsa ya ɗauko ya ɗauki system ɗin buɗewa yayi direct folder daya buɗema Amal ya shiga ya fara karanta irin texts masu daɗin da take tura masa lokacin yana makaranta, murmushi yayi tabbas nasan kina sona Amal kuma nima ina sonki bazan ta'ba jure rabuwa dake a daidai wannan lokacin ba koɗan farin ciki da zumuncin iyayen mu, nayi alƙawarin zanci gaba dayi miki addu'ah har lokacin da Allah zai nusar dake gaskiya," Ina ƙaunarki sosai Yar' uwata banada burin daya wuce na kasance dake har abada, rungume system ɗin yayi ya jingina jikinsa da kujera ya nausa cikin duniyar tinani.
Mee'ad tin ƙarfe takwas suka tashi bayan sunyi wanka ta nufi ɗakin Hajiya Hindu domin kar'ban kuɗin ankon da tayi mata alƙawari, zaune ta tarar da ita bisa sallaya tana jaan casbaha zama tayi bisa gado tana jiranta,"
Ta shafa addu'ah barka da safiya Takwarata yau naga kina cikin farin ciki sosai, ko angon namu yayi miki kyautar kuɗi ne ? Murmushi Mee'ad ɗin tayi au dama har wani ango ke gareki Hajjaju ? Kinga kwantar da hankalinki da wannan zolayar ki tashi ki ɗauko kuɗin anko ki miƙo! domin tin ɗazu muka shirya ke kaɗai muke jira," Kinga na manta da zancen anko ma tashi ki buɗe wancan drower zakiga ƙaramar jaka ki ɗauko saina baki," Fuskarta cike da farin ciki ta ɗauko jakar ta miƙa mata gashi Hajjaju ki hanzarta domin ke kadai muke jira, Tayi murmushi kafin ta buɗe jakar yan dubu ~ dubu ta ɗauko ta ƙirga 20k ta miƙa mata gashi ki sayi duk abunda ranki yakeso, Allah ya kiyaye hanya. Ta kar'bi kudin tayi godiya kafin ta fice daga ɗakin tana murmushi.
"Kai tsaye Amal ɗaki ta nufa fuskarta cike da takaici, kwanciya tayi bisa gado ta fara tinanin hanyar da zatabi a fasa aurenta da Majeeed ɗin domin ta tsaneshi bata ƙaunarsa tin lokacin da taga wanda ya fishi kyau da komai da rayuwar duniya taji baki ɗayan hankalinta ya koma kan wancan ɗin," wayarta ne tayi ring ta duba screen dan ganin waye yake damunta da waya tin ɗazu, Murmushi tayi datayi arba da sunan Areeef rubuce a fuskar wayar, kara wayar tayi a kunnenta tace hello freind yayane ? Murmushi  yayi wanene freind ɗin nifa tin jiya na tashi daga freind na koma masoyi domin na yabada dukkan tsarinki keɗin ta musamman ce kuma keɗin zazzaface ta ƙure tinani,"
"Tayi juyi fuskarta cike da annuri Au tsokanata kakeyi ? Ka manta da rayuwar da kayi da fararen fata waɗanda suka fini kyau da gayu nesa ba kusa ba," 
Hmmm Amal kenan tin lokacin da nayi arba dake zuciyata ta ƙware a kanki nayi niyyar faɗa miki a lokacin sai dai kash kin fiye jaan class da yawa duk rigimata sai naga kin fini wannan dalilin ne ya sanya na kasa baiyanar miki da komai akan lokaci but now na faɗa miki da ƙarfin zuciya kuma cike da yaƙinin zaki amshi tayin da na miki," 
Ta ɗanyi jim kafin ta gyara zama Areef bazan ta'ba cewa baka burgeni ko bakayi mini ba saboda kaiɗin na musamman ne wanda kayi nasarar tafiya da baki ɗayan zuciyata kuma a lokacin da banyi tsammanin hakan ba , ta ƙarayin shiru kafin taci gaba Areef kayi haƙuri da abinda zan faɗa maka saboda faɗa maka yana da matuƙar muhimmanci Areef jiya Uncle ɗina ya yanke ranar aurena nan da 4weeks kuma bai zama lallai ya canja abunda ya yanke ba, duk da nasan yanda matuƙar sauƙin kai kuma yanason abunda mukeso,"
"Areef yayi shiru kamar wanda ruwa ya cinyeshi kafin daga bisani yayi gyaran murya Amal ki kwantar da hankalinki ina sonki sosai kuma zuciyata ta gama amincewa da son da nakeyi miki, Amal ina ba ɗaura aurenki akayiba ? To tinda ba ɗaura aurenki akayiba bazan taba janye soyayyarki daga zuciyat ba, zan iya jurar duk wani wulaƙanci dacin zarafi idan har akankine, jiya bayankin shiga gida munyi magana da wani........nan ya bata labarin yadda sukayi da Daddy.
Muryarta a sarƙe tace haka kayi da Daddyn ? Na shiga uku Areef kaine ka janyo aka sanya ranar aurena yanzu yaya kk so nayi ? Wallahi banison Yaya Majeeed yanzu.
Kinga ki kwantar da hankalinki zan faɗama Mom ɗina duk yadda mukayi dake kuma inada tabbaci akan zataso aurena dake kuma zata iya zuwa har gidanku ta bama Daddy haƙuri domin auren mu ha kasance,"
Taja dogon numfashi Areef bakasan halin Daddy da magana ɗaya bane baki ɗaya bayison canza magana idan har yayi," amma bansan kozai amince da maganar Mom ɗinka ba, nan sukaci gaba da tattaunawa.
Hajiya Suwaiba ce zaune a falo tana kallo, Amal ce ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi Umma barka da wannan lokacin, barka dai Mamana ya naga fuskarki sai ƙyalli takeyi kamar sabuwar Amarya,"
"Murmushi tayi hmmm Ummana kenan nazo miki da wani sabon albishir,"
"Wow kice na gyara zama kuma na karkaɗe kunnuwa na da domin saurarenki.
"Dariya ta fashe dashi kafin tace Umma ɗazu munyi waya da Areef........ta lissafa mata yadda sukayi.
"Murmushin jin daɗi mai haɗe da farin ciki Umman tayi Allah yayi miki albarka ɗinyar arziki, banida hanci da nayi guɗa dan farin ciki Allah ya tabbatar da alkairi ya kuma haɗa kanku keda sabon masoyinki iri wannan kyakkyawan haɗin daɗi gareshi kai masha Allah, kinga yanzu o da Majeeed ya gama zama tari..........bata ƙarasa faɗar maganan ba tayi ido huɗu da Majeeed tsaye cikin falon fuskarsa babu annuri.
pls 
Follow 
Share
Vote
Comment
Fisabilillah.