HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Sha Bakwai

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Da Cin Amana Mafi Muni, Fita Ta Sha Bakwai

   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 


          Page 17


Mutanen gidan suka taso hankali tashe ganin Abban Haidar an tabbatar da ba lafiya ba. Ni kam ina biye da mutane ko a jikina, ji nake tamkar ba abin da na aikata don haka ko shakka babu a fuskata balle a ga razana, ko hakan da aka gani ne yasa mahaifiyarsa kama sunana tana tambayar abin da ya sami ɗan nata oho. Nikam na yi shiru don ban san me zan ce ba, nasan dai a tunanina kowa ya ji sanadin faɗan ba za ace ban kyauta ba, saboda babu wanda bai san darajar mahaifansa ba. Mijin Binta ya gaya masu faɗa ne mu kai da shi har hakan ya faru, nan da nan sai kallo ya komo kaina, mamaki ƙarara kan fuskar kowa. Ban ankara na ga kowa ya maida fuskar shanu kan ta mamakin da suka shiga da jin labarin nice da kaina na ba shi kashi har bai iya taka ƙafarsa. Cikin gaggawa aka kirawo mai gyara, macece, ta taɓa ƙafar tace, "Wannan ai tsagewar ƙashi ce, halan wajen ƙwallon ƙafa ne ya je aka sabauta shi haka?"  Sai kowa ya yi shiru ba wanda ya amsa mata balle ya ƙara mata bayanin inda ya je ya tsago ƙashin ƙafarsa. Sai da aka nemo majiya ƙarfi suka riƙe Deeni sannan aka gyara ƙafar aka ɗaure wajen da ƙashin ya tsage. Sai ihu yake yana kuka yana hayagaga kamar ƙaramin yaro, gidan ya cika da mutane ana ta mai sannu, wasu na nuna ni, ko ban tambaya ba nasan cewa gulmar dukan da nai ma Deeni ake yi.

Bayan an gama yi mai gyaran, mutane sun watse sai matan gidansu, suka taro kansa suna cewa, "Daga Yau kar ka sake ka sake haye mata, don wannan tana iya kashe ka a banza. Kai dai da tai maka laifi ka je gun iyayenta ka gaya masu su ne za su ɗaukar maka mataki kanta, tunda ta fara da haka watarana karya maka ƙafa ko hannu zatai." 
Ni dai ina zaune Ni da Haidar sai binsu mu ke da kallo bance komai ba. To me zan ce? Ni dai nasan tabbas zan iya auren rashin abinci rashin sutura amma ban auren zagi da duka.

Ganin ba mai min magana yasa na kama hannun yarona muka nufi gida. Ina zuwa zaure naji ana cewa, "Ku ji munafukar yarinya a haka kamar saliha ace muguwar gaske ce, ta ƙin ƙarawa, to wallahi kada ka sake ka sake haye mata duk yadda zata tsokane ka ta neme ka da masifa wallahi ka kiyayi kanka kai banza da ja'ira ka bar mata gidan kai tafiyarka ta bugu wani ba dai kai ba."

Na taɓe bakina cike da mamakin me yasa basu tambayi abin da ya haɗa faɗan ba? Me yasa shi kawai suke ba gaskiya da shawara ban da Ni? Ganin ban da amsar na wuce gida hankalina kwance, nasa a raina ya wuce kuma har a zuciyata ko ya dawo ba zan tada maganar ba.

Ina zuwa unguwarmu naga mutane nata kallona, masu son jin gulma suka bini har cikin gidana, suna tambayata "Wai Jiddah me ya haɗa ku da Deeni ne Yau Allah Ya baki ƙatuwar sa'a kan shi?  Wata tace, "Wallahi Jiddah kin nuna ma shi ke ɗin mace ce ai nasan wallahi shi ne ya kai ki ƙarshe, don sai dai mutum ya ƙi Allah indai kan zamanki da Deeni ne kowa yasan zaman haƙuri kawai kike da Deeni."
Ni dai ban tanka ba, domin dai babu amfanin tankawar, kawai ji nayi ba zan lamunci zagin da ya yi min ba, ganin ban da niyyar bayyana masu asalin abin da ya haɗa mu faɗan, yasa kowacce ta zare jikinta ta fice, aka bar Ni da Binta kawai zaune. Bayan sun fita Binta ta dube ni da alamar sanyin jiki tace, "Yanzu ke Jiddah kina ganin abin da ki kai kin kyauta kuwa? Baki tunanin idan ya warke ya yi maki wani mugun abun? Wallahi Jiddah ban ji daɗin abin nan ba, saboda Deeni bai da tausai haka Allah kawai yasan me ya saka a ransa a kanki yanzu, don haka ki yawaita addu'a sosai Allah Ya yayyafawa fitinar ruwan sanyi."
Na dube ta har zuwa lokacin fuskata babu alamar damuwa nace, "Binta wai kema kin damun ne? Koko kema laifina kike gani? To wallahi ni har cikin raina ban jin komai haka ban damu ba, saboda nasan ko a gaban wa aka maida yadda akai ban da laifi shi ne ya take girmansa ya nuna min bai san darajar Iyaye ba Ni kam nasan darajar iyayena don haka na rama." 
Binta nata kallona kamar ta samu talabijin tace, "Wallahi kuna tafiya ihu aka dinga yi a cikin unguwar nan ana cewa garama hakan, wasu cewa su kai dama kin kakkarya shi yadda zai jima bai samu ƙafafun jawo maki mata cikin gida ba." Sai abin ya ban dariya, don haka na dara, Haidar ganin ina dariya shi ma ya saka dariya, tamkar ba wata matsala haka nake jina don haka raina fes Binta ta fice ta barni ina wasa da Haidar.


Dare nayi na shirya Haidar na koma gidansu Deeni don tabbatar da zai dawo gidan ko bai dawowa? Idan bai dawowa na samu waje na kwanta idan an barmu idan ba a barmu ba sai na ɗauko Yarona na dawo gidana na kwanta.
Ko da na isa na iske yana kwance yana latsa wayarsa ko ban tambaya ba nasan chat yake, na duƙa har ƙasa na gaida Mamarsa da mutanen gidan, sun amsa dai amma irin can cikin zuciya ɗin nan.
Na dubi Deeni nace, "Ina wuni ya jikin naka?" Idan bangon ɗakin ya tanka to shi ma ya tanka, don haka ni ma na share kawai na sadda kaina ƙasa ban sake cewa komai ba.

Haidar ya nufi gun Babansa yana gwarancinsa, Kakarsa tai wuf ta janye shi da zuwa inda Deenin yake tace, "Don Uwaka kai ma baƙin halin da baƙar zuciyar ce ta gado ta motsa ko da zaka je ka fama mai rauni? Yaro tun kana ƙaraminka ka iya mugunta? To wallahi baka ji daɗin halinka ba, indai kai gadon mugun hali an tsotsi baƙin nono ba inda zaka je a cikin dangi ka ji daɗi."  Ni dai kaina na ƙasa na fahimci magana ce take gayamin, don haka nayi tamkar ban gun.

Haka na zauna tsawon lokaci sai dai na tashi nayi sallah na dawo na zauna, gabana aka gama abinci ba a ban ba ina gani aka ba Deeni ko kallonmu bai ba ya ci, Haidar ne ma abinka da yaro ya nufi gun Uban yaga yana cin abinci, ya kuwa daka mai tsawar gaske har ya ruɗe ya fashe da kuka, na kama Yarona na rungume ina lallashinsa na samu ya daina kukan cikin sa'a barci ya ɗauke shi.

Haka na ɓata awanni ba wanda ya yi min magana , balle ya yi fira da Ni. Ganin dare ya miƙa ba wanda yace min ga wajen kwanciya ga barci ina ji, har ma da yunwa yasa na tashi tsab na goya Haidar, na waiga naga kowa ya yi barci har shi kanshi Deeni ya gaji da chat ɗin ya yi barci, sai na ji raina ya ɓaci wannan wulaƙanci ne don haka bakina a laikum na fice daga ɗakin na nufi gidana, ina zuwa zaure naga har an rufe gidan, na buɗe ban ji komai ba na fice garin ya yi tsit ba haske don ba nepa, na waiga gabas na waiga gudu da arewa ban ga kowa ba, na kama hanya zan tafi kenan duk da ban da hitilar haskawa amma na dakewa zuciyata na raya a raina Yau komi zai faru sai na kwana gidana cikin mutunci.

Kamar daga sama naga wani irin dogon mutum gabana mai wani irin tsawon gaske, da wata irin fitila mai hasken gaske. Ya haska kayan jikinsa naga sak irin kalar kayan dake jikina ne, amma ban iya hango kansa ba, bai min magana ba, kawai ya shige gabana yana haska fitilar Ni kuma kamar ance na bishi baya haka na bi shi duk inda ya cire ƙafa ina maida tawa.
Haka mu ka tafi har ƙofar gidana, mutumin na gabana ina bayansa, kuma Ni ban ga kanshi ba, kawai tsawonsa nake gani Ni dai. Na buɗe gidan na shiga bai tanka min ba nima ban tanka mai ba, sai da na shige gidan na buɗe ɗaki na maida na rufe kawai naji wani irin tsoro ya dirar min, nan da nan jikina ya tsinke da kyarma, na samu da ƙyar na sauke Haidar dake bayana a tsakiyar falon na duƙe ina dafe da kaina jikina baki ɗaya ban da kyarma ba abin da yake.


To masu karatu mu haɗu a kashi na gaba don jin me zai wakana ga Jiddah.

Taku a kullum Haupha