Abin Da Babba Ya Hango:Fita Ta Shida

Sosai suka ji daɗin hulɗar su da Zuly duk da wannan ne karo na farko, ko bayan dawowarta hayyacinta bata ji komai ba saima burgeta da abin yaci gaba da yi, tun daga ranar basu da aiki sai aikata ɓarna, da sunci sun ƙoshi suka kwankwaɗi kwayoyin su sai kawai su faɗa.......

Abin Da Babba Ya Hango:Fita Ta Shida

ABINDA BABBA YA HANGO.......!

RUBUTAWA; DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.

FITOWA TA SHIDA.


Kwanansa uku a gidan yana  shan ruwan addu'o'in da Malam Nasiru ke aiko masa safe da rana da maraice, sosai yake jin kamar ƙullin dake gabansa yana kwance wa, harya fara jin safai da shi, duk da haka kuwa duk bayan kwana uku sai an kawo masa rubutun tsarin jiki.

Sai da ya yi sati biyu a gidan har wannan karon ba ZULFA'U ba labarinta ko nemansa a waya ba ta yi ba, a ranar daya cika 2weeks ranar ya fara zuwa aiki, sosai ya taradda ayukka birjik a gabansa bugu da ƙari kayan da suka yi order sun iso tun last week dan m Bash abokinsa yana kula da wadansu abubuwan.

Yinin ranar kacokan a office ya yi sa, yana tashi kuwa ya wuce gidansu, sosai abinda ya faru da shi a baya ke damunsa har kunyar haɗa idanuwa da su Hussaina yake ji uwa uba Maimunatu wacce mafi yawon lukutta a sashen nasu take wuni tare da su 'yan biyu dama su ne kaɗai ƙawayenta.


A ranar da suka fice daga gidan kai tsaye club suka nufa , suka sha suka ƙoshi kana suka wuce gidan Hajiya Turai.

Tun a Parlour suka fara aikata masha'arsu su biyu Ruka da Turai Zuly na gefe tana kallonsu duk da ba cikin hayyacinta take ba amman abin na matukar baƙanta mata rai.

Ta runtse idanuwanta kenan koda ta buɗe ta gansu a gabata a lokacin ne ta ji kamar ana ƙara tunkuɗa ta a kansu ba shiri ta faɗa cikinsu suka ci gaba da aikata muguwar ɗabi'arsu.

Sosai suka ji daɗin hulɗar su da Zuly duk da wannan ne karo na farko, ko bayan dawowarta hayyacinta bata ji komai ba saima burgeta da abin yaci gaba da yi, tun daga ranar ba su da aiki sai aikata ɓarna, da sun ci sun ƙoshi suka kwankwaɗi kwayoyin su sai kawai su faɗa.......

Wa iyazu billah! Ubangiji Allah ya tsare mana imanin mu ya karemu da aikata aikin dana sani, Allah ya kare mu da miya gun ƙaddarori, Amin ya Allah.

Cikin ƙanƙanin lokaci Zuly tayi fice a harkar su ta neman jinsi da jinsi.

Kasancewarta ta fisu diri da komai ya sanya cikin ɗan ƙanƙanin lokaci duk wacce ke wannan harkar tasan da ita.

Sai da ta yi sati uku sannan ta dawo gida, taci ka da mamakin ganin baya gidan daga baya kuwa ta yi watsi da lamarin.

Zaune take a Parlour ƙafa ɗaya kan ɗaya, wayarta dake riƙe da hannunta ne ta hau ruri ganin me kiran ne ya sanya ta saurin miƙewa tsaye tana fiddo da idanuwa waje , gaba ɗaya ta manta da sunyi magana da Haruna kan za ta bashi kuɗi sai yanzu data ga kiransa.

Bedroom ta nufa ta janyo veil da jikkarta ta nufi waje.

Key ta yiwa motar ta nufi hanyar gidan Haruna tana mai addu'ar Allah yasa lafiya don tun ɗazu yake faman kiranta a waya.

Bakin ƙofar gidan tayi parking ta fito da sauri ta faɗa gidan.

Suna zaune a tsakar gidan ya yinda Baby ke kwance ba lafiya , matar Haruna sai fifita take yi mata, shi kuwa waya ce a kunnensa yana ƙara danna mata calling.

Ganinta kawai suka yi ta faɗo gidan yana tambayar lafiya kuwa.

A tare suka miƙe, maryama na yi mata barka da zuwa tana mai shimfida mata tabarma a gefen wacce Baby take sama, ya yinda shi kuwa ya murtuƙe fuska kamar be taɓa dariya ba.

"Ka zauna mana Haruna ka yimin bayani mi ya sami Baby?", ya faɗa yana mai taɓa jikin yarinyar dake bacci.

"Ke zan tambaya ai, fisabilillahi kin kyauta mana kenan?, Yau kusan wata biyu fa ina nemanki amman gaba ɗaya kinyi watsi da mu, tun last week nake neman layin ki bana samu sai yanzu dana je gidan Turai ta bani new number ki".

"Ka ga Haruna ba wannan ba meke damun Baby?".

"Zazzaɓi ne mai zafi ya rufe ta na kaita asibiti suka rubuto maguna to babu kuɗi hannuna ban samu siyo ba."

"Ɗauki min takardar naje na siyo", ta faɗa tana zuge zip ɗin jakkata.

Kuɗi ta ɗibo 10k ta bawa Maryama tana faɗan "a yi haƙuri dasu", kana ta ɗauko 70k ta miƙawa Haruna, "hamsin wadanda ka ce, ashirin kuwa ka saye ɗan wani abu, idan na fita zan dawo da maganin."

Jikinsa na rawa yasa hannu biyu ya ƙarɓa suna ta zuba godiya a gareta.

Ficewa ta yi daga gidan taje siyo maganin.

Bata jima ba kuwa sai gata da maganin da kayan abinci niƙi niƙi, haka su Haruna suka dinga yin godiya sosai da sosai.

Sai da ta jawa Haruna kunne a kan ya kula da Baby sosai duk abinda take so ya hanzarta kiranta idan tana ƙasar za ta zo idan bata nan za ta aiko mata da shi.

Har bakin motar ta ya rakata sannan ya dawo cikin gida yana murna anan suka game da Maryama suka ci gaba da farinciki.


Idanuwan ZULFA'U sun buɗe sosai da harkar neman 'yan uwanta mata haka kuma har yau tana tare da Alhaji  Sambo wanda ke yi mata ɓarin nera.

Yau suna tashi daga club kai tsaye gidanta suka nufa, tun a Parlour suka fara aikata masha'arsu su biyu ne wannan karon ita da Hajiya Turai, sosai suka shagala har basu san lokacin daya shigo gidan ba.

Jin gurnani kamar na dabbobi ya sanya sa saurin shigowa Parlourn sai dai me? .

Abinda ya gani ne ya yi masifar tada mashi da hankali, jikinsa har tsuma yake yi yayinda idanuwansa suke fitar da hawayen takaici da kuma mugun ganin da ya yi da su.

Juyawa ya yi ya fice daga Parlourn yana mai sa key ya kulle su , bayan gidan ya nufa ya cire rigar jikinsa ya wurgar da ita kana ya hau iccen darbejiya ya tsinko sa da yawan gaske kana ya sauko kasa.

Kai tsaye Parlourn ya koma har lokacin suna nan yadda ya barsu, rufe idanuwansa ya yi kana ya tunkare  su gadan gadan.

Jin duka kawai suka yi a bayansu ba shiri suka rabu da juna, sai neman agaji.

Sai da yayi masu lilis dukkanin fatar jikinsu saida ta kwalɗe sannan ya barsu.

Ɗakinsa ya nufa ya ɗauko biro da talkarda ya rubuta mata saki uku kana ya dawo ya wurga mata taƙardar yana faɗan "ki je na sake ki saki uku bani ba ke macuciya, makirar Allah wacce bata tsoron Allah, Ubangiji Allah ya yimin sakayya dake ba zan taɓa yafe maki ba!."

"Kinsa na bijirewa iyayena , na tabbata da badan ruɗina da kika yi ba, da bazan taɓa bijirewa iyayena ba, ki je Allah ya fiki, dama Hausawa sun ce " ABINDA BABBA YA HANGO YARO KOYA HAU TSAUNI BAZAI GANSHI BA!,Irin abinda iyayena suka so nunamin kenan game da ke, amman da yake kin riga kin gama dani a lokacin bana ji bana gani , naƙi 'yar uwata na zaɓe ki sai gashi kin nunamin halin naku na karuwai."

Ganin ta tsaresa da idanuwanta tana ci gaba da kuka ne ya sanya shi zare mata idanuwa "yace dan gidan ku ki daina kallona tunkan na ƙara maki wani, ki yi maza ki tada wannan almurar daga nan ku fice min daga gida tun kafin na aikaku police wallahi."

Jikinta na rawa ta hau tada Hajiya Turai wacce ta suman wahala.

Sai da ta yayyafa mata ruwa kana ta farfaɗo ba shiri suka kwashi 'yan abinda ba'a rasa ba suka yi gidan Hajiya Turai.....

Za mu ci gaba Gobe...............

ƳAR MUTAN BUBARE CE.