NSA Ya Mika Dalibai Dari Da Aka Ceto Ga Gwamnatin Jihar Neja
Mai Ba Da Shawara kan Tsaron Ƙasa (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya mika dalibai 100 na makarantar St. Mary Catholic School da ke Papiri, karamar hukumar Agwara a jihar Neja, ga gwamnatin jihar bayan ceto su daga hannun masu garkuwa da mutane.
An gudanar da mika su a Minna a ranar Litinin, inda Wing Cdr. Abdullahi Idi Hong ya wakilci NSA wajen gabatar da su ga gwamnatin jihar.
Hong ya ce ceton ya biyo bayan makonni na tsauraran hare-haren hadin gwiwa tsakanin Ofishin NSA, Hukumar DSS, Rundunar Sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro. Ya bayyana cewa DSS ta taka “muhimmiyar rawa ta zahiri” a aikin da ya tabbatar da dawowar yaran cikin koshin lafiya.
Ya kara da cewa ofishin NSA ya fara aiwatar da matakan gaggawa na tsaro a yankunan da ke fuskantar barazana, tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi, shugabannin gargajiya da na addini domin samar da tsarin tsaro mai dorewa.
Hong ya jaddada cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da ke nufin tabbatar da tsaro a makarantu da kare hakkin kowane yaro ya sami ilimi cikin kwanciyar hankali.
Da yake jawabi, Gwamna Umaru Bago ya bayyana wannan rana a matsayin “muhimmiya a tarihin jihar Neja,” inda ya gode wa Shugaba Bola Tinubu bisa tallafin da ya bai wa hukumomin tsaro.
Haka kuma ya yi godiya ga NSA, jami’an tsaro, hukumomi da al’ummar jihar da suka yi addu’o’i a lokacin da yaran ke tsare.
Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwa cewa sauran daliban da har yanzu ke hannun masu garkuwa za a kubutar da su ba da jimawa ba.
Ya tabbatar wa iyaye cewa za a mika yaran ga iyalansu bayan cikakken binciken lafiya.
managarciya