BABBAN BURI
MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.
SADAUKARWA GA A'ISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}.
FITOWA TA ASHIRIN DA HUƊU
"A madadin wannan kotu mai adalci ta yankewa Alh Bello da Alh Murtala hukuncin zaman gidan horo na kimanin wata biyar tare da horo mai tsanani, kana daga bisani a yi masu kisa ta hanyar rataya!."
Kotu ce ta ɗauki maganganun mutane kowa na faɗin albarkacin rayuwarsa ya yin da matan su Alh Murtala da ƴaƴansu suka rushe da kukan baƙin ciki.
Alƙali ne ya tsawatar kana al'umma suka sarara daga bisani yaci gaba da cewa "ƴan uwansu kuwa wanƴanda da taimakawar sune aka aiwatar da wannan kisan cin mutuncin zuwa ga Musulmi wannan katun ta yanke masu ɗaurin rai da rai a gidan horo kana da horaswa mai tsanani!."
Nanma sai da kotu ta ɗauki maganganun mutane da kukan waƴansu makusantan su.
Kana daga ƙarshe kotu ta tashi.
Waƴansu na kuka waƴansu kuwa najin daɗin hukunci da aka yankewa waƴannan bayin Allah.
Mu dai ayarinmu ba zaka taɓa gane menene a zuciyarmu ba, domin kuwa ba zamu ce muna farin cikin wannan hukunci ba ko akasin hakan kasan cewar ko bakomai ƴan uwanmu ne na jini.
Lokacin da muka fito daga kotu ƴan jarida suka yo mana caaah, akai kowa nason yaji ta bakinmu sai dai hakan bata samu ba, ɗaya daga cikin ƴan jarindan dake cikin jahar Sokoto ne ya wurgo mana tambaya yana me tare gabanmu sannan ya kara mana abun mgna a bakinmu "Malama me zaki iya cewa a game da wannan Shari'ar, abin nufi kina farin ciki da wannan hukunci da kotu mai adalci ta yankewa waƴannan bayin Allah ko kuwa akasin hakan?."
Kallonsa na yi haka kawai naji bazan iya wuce wa na ƙyalesa ba sannan na ce "ba abinda zance anan sai dai ince Allah yasa hakan shine alkheree, masu irin waƴannan halayen Ubangiji Allah ya shiryar dasu damu gaba ɗayan mu."
Kana na ratsa ta gefensa na wuce.
Gurin dasu Baba Bello suke tsaye muka nufa , kai tsaye Baba yaje ya rungume su su dukansu ya fashe da kuka, su kansu kukan sukeyi me taɓa zuciya".
A haka dai muka rabu rai babu daɗi , muka nufi gida ko wanne da abinda yake saƙawa a cikin ransa.
Haka gidanmu ya koma kwana biyu kamar gidan mutuwa .
A lokacin mutuwar ta dawo mana sabuwa dall.
*Bayan wata biyu.*
Zuwa lokacin komai ya wuce a gurinmu sai ɗan abinda ba'a rasa ba, mun koma rayuwarmu irinta daah, ya yinda matan gidan suke zaune a cikin gidan namu har yanzu, duk da Ya Haidar yaso su bashi gidansa a cewarsa hwa, amman Baba ya hana sa a cewarsa a ina zasu zauna idan ya ta dasu?."
Bayan mun gama cin abinci dare muna zaune mu dukanmu , Baba ya fito da kuɗi daga cikin aljihunsa kana ya kalli Hajiya Inna ya ce " ga kuɗin neman aure mun bayar muna buƙatar iri daga gare ku.".
"Hhhhhhh" dariya muka sanya gaba ɗayanmu harshi kansa Baba domin kuwa abin ya bawa kowa mamaki harda yadda ya yi zancen.
Ni dai muna gama dariya na yi maza na miƙe na bar sashe na Hajiya Inna na nufi sashen Mama.
Bansan yadda aka isala ba, na daiji A'isha na maganar an sanya rana wata biyu masu zuwa, nan da sati ɗaya zamuje ƙiri daga can mu wuce Wurno domin a sanarwa da mutane lokacin bikin.
Bayan Mama ta shigo sashen ne ta kalleni ta ce "tau an sanya rana hankali ya kwanta , sai kiyi taka tsantsan domin kuwa yanzu sheɗan zai dinga kawo maku hari sai a kiyaye Allah ya tsare ya nuna mana lokaci."
A cikin raina na amsa da "Amin ya Allah".
★★★★★★
Yau da murnar zuwa ƙiri muka tashi ko wannen mu murna fal kwance a saman fuskansa, cike muke da farin ciki kasan cewar an kwana biyu ba'a tafi ko ina ba muna kulle a cikin gida ko yaushe hakan ya sanya kowa ka kalli fuskansa zaka tabbatar da ɗaukin tafiyar a tare dashi.
Ƙarfe 7am motar mu ta ɗaga zuwa ƙiri 1hour mukayi a saman hanya kana muka isa gidan Malam.
Damu har Mama mun cika da ɗumbin mamakin ganin yadda aka canjawa gidan samfari gaba ɗaya ya koma gidan ƴan gayu ba zaka taɓa cewa shine gidan lakannan ba.
Mamakin mu kasa ɓoyuwa ya yi lokacin da muka shiga cikin gidan domin kuwa komai an canja shi, harma da ƙarin sauye sauyen da aka samu.
Daga shigowar ka gidan zaka ci karo da ɗakin Gwaggo dana Malam, suna kallon ka, daga daman sa kitchin ne tare da banɗaki ,sai kuma daga hagunsa wurine aka killace da gini daga ganinsa zaka tabbatar da ɗakine a gurin sai ban ɗaki da kitchin.
Zaune mukayi a saman shinfiɗar da Gwaggo ta yi mana muna masu gaidata.
A haka muka dinga yawon gaida ƴan uwa da abokanan arziƙi, duk gidan da muka shiga kuwa sai sun bani tasu gudummawa ta kayan mu na mata, damamin sukeyi da kansu irin namu na gargajiya ne a bani a tsareni saina shanye.
Tun abin baya damuna harna fara jin canji a jikina , ƴan kwanakin da muka yi a garin harji na yi gaba ɗaya bana ra'ayin zaman sa, badan komai ba kuwa sai don irin kayakkin da ake ɗuramin a ko wacce safiya.
A ranar da zamu bar garin zuwa Wurno kuwa ba ƙaramin daɗi naji ba ko bakomai Allah zai hutar dani, ashe ban sani ba wani ƙara'ine ke kirana.
In taƙaice maku ko a Wurno ba aba barni na huta ba, ɗuramin kawai suke yi, bani da halin ƙinsha domin kuwa tsareni a keyi saina shanye na bayar da kofi.
Ai kuwa sosai na canja cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, nayi jiki sosai fatarnan tawa kamar ka taɓa jini ya fito gwanin sha'awa.
A haka muka juyo muka dawo gida ɗauke da kayan tsara ba niƙi niƙi.
A haka muka baje Parlourn Hajiya Inna muna bubbuɗe komai da komai.
Sharye shiryen biki kaɗai mukeyi ba kama hannun yaro, yauma ina zaune a sashen Mama ta shigo har cikin ɗakin daya ke namu ta zauna cikin hikima take nunamin abubuwa waƴanda ba lallai bane na sansu haka kuma a cikin hikima take yimin nasiha game da zaman aure sosai komai ke shiga cikin kaina, daga ƙarshe ta rufe dayi mana addu'ar samun zaman lafiya da haƙuri da juna.
A haka muka ci gaba da gudanar da komai ni da ƙawata Fateema, duk da ba waƴansu abubuwane za muyi da yawa ba, wankin amarya ne shi dama ya zamto al'ada sai ranar cin kwai da kwai {awara} sai walima sai kuma dinner da abokanan Ya Haidar suka shirya masa a daren ranar da za akai amarya.
Amman komai sai tsara yadda zamu gudanar dashi mu keyi.
Haka ma a gefen ango ma bashi da hutu tun lokacin da muka dawo daga Wurno ko wacce safiya yana gurin ganin an kammala ƴan gyare-gyaren da ba'a rasa ba a gidan da za'a kai amarya.
Ba ƙaramin ta nadi yayi wa bikinnan ba.
Haka ma Baba shi kansa ba zama yake samu ba, domin kuwa yanzu ayukka duk sun kaca me masa a gurin aiki Kasancewar Shalelen Hajiya Inna ba zama yake samu ba...........
ƳAR MUTAN BUBARE CE