Jagororin PDP suna lallaɓar Mark da Maƙarfi da Sule Lamiɗo a shugabanci jam'iya

Kafin yanke hukuncin 'yan takara ne daga Kudu suka nuna sha'awarsu ta tsayawa takarar shugaban jam'iya.

Jagororin PDP suna lallaɓar Mark da Maƙarfi da Sule Lamiɗo a shugabanci jam'iya
Jagororin PDP suna lallaɓar Mark da Maƙarfi da Sule Lamiɗo a shugabanci jam'iya

Wasu jagorori a jam'iyar PDP sun fara lallaɓar tsohon shugaban majalisar dattijai David Mark da tsohon gwamnan Kaduna Ahmed Maƙarfi da tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido kan su amshi shugabancin jam'iyarsu.
Lissafin ya canja bayan da kwamitin karɓa-karba ya tura takarar shugaban ƙasa a Arewacin Nijeriya.
Kafin yanke hukuncin 'yan takara ne daga Kudu suka nuna sha'awarsu ta tsayawa takarar shugaban jam'iya.
Jam'iyar ta sanya zama na gaggawa a ranar Alhamis kamar yadda sakataren jam'iya Umaru Ibrahim Tsauri ya sanar.
Ba a sanar da maƙasudin zaman ba amma dai ana sa ran amincewa ne ga aikin kwamiti.
Za a kuma tattauna kan kwamitocin babban taro na ƙasa na mutum 279 da gwamna Ahmadu  Umaru Fintiri ke jagoranta.