Jagororin PDP a Arewa maso yamma sun yi zaman ɗunke ɓarakar da yankin ke fama da ita

Yankin na fama da rikicin shugabanci tun bayan da aka kasa gudanar da zaɓen shugabanni a yankin in da rashin fahimta ya kunno kai a tsakanin Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso kan zargin Tambuwal ya yi katsaladan a kujerar da aka baiwa jihar Kano

Jagororin PDP a Arewa maso yamma sun yi zaman ɗunke ɓarakar da yankin ke fama da ita
Jagororin PDP a Arewa maso yamma sun yi zaman ɗunke ɓarakar da yankin ke fama da ita

Jagororin PDP a Arewa maso yamma sun yi zaman ɗunke ɓarakar da yankin ke fama da ita

Jagororin jam’iyyar PDP a Arewa maso yamma sun yi muhimmin zama a gidan Tsohon gwamnan jihar sokoto Alhaji Attahiru Bafarawa a Abuja domin shirye- shiryen samun nasara babban taron da jam’iyyar zata gudanar a watan Okotoba.

 
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Muhammad  Namadi Sambo ya jagoranci zaman wanda mafi yawan jagorori a yankin sun halarta tare da shugabannin jam'iya a jihohin yankin.
Yankin na fama da rikicin shugabanci tun bayan da aka kasa gudanar da zaɓen shugabanni a yankin in da rashin fahimta ya kunno kai a tsakanin Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso kan zargin Tambuwal ya yi katsaladan a kujerar da aka baiwa jihar Kano.
A lokacin rashin fahimtar ta hana a yi zaɓen da aka shata gudanarwa a Kaduna abin da ya sa uwar jam'iya ta kafa kwamitin riƙon kwarya kafin a yi silhu a yi zaɓe.

A halin yanzu lokacin zaɓen ya zo don ba makawa sai yankin ya samar da shugabanni kafin babban taron ƙasa kuma zaɓe ba zai yiwu ba in har ba a samu daidaiton jagororin ba.
Managarciya ta fahimci zaman nada nasaba ne da ɗunke ɓarakar dake tsakanin Tambuwal da Kwankwaso bayan batutuwan babban taron ƙasa.