Mahaifin Kakakin Majalissar Dokokin Zamfara Ya Rasu A Hannun 'Yan Bindiga
Alhaji Abubakar, mahaifin kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Honarabul Nasiru Magarya ya mutu yayin da yake a tsare hannu masu garkuwa da mutane.
Mahaifin Kakakin wanda shi ne Hakimin ƙauyen Magarya, 'yan bindiga sun yi garkuwa da shi makonni takwas da suka gabata, tare da matarsa, da kuma jariri dan makonni uku da hai huwa.
Yayin da aka ceto wadanda aka sace a jiya Asabar, mahaifin kakakin Majalissar baya cikin su.
Kazalika da yake jawabi ga manema labarai, babban yayan mamacin, Malam Dahiru Magarya, wanda yana cikin wadanda aka sace ya ce, mahaifin kakakin Majalissar ya rasu ne a hannun Yan bindigan, sakamakon bugun zuciya.
Sai dai har kawo hada wannan rahoto majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Gwamnatin jihar da rundunar ‘yan sanda har yanzu ba su yi magana kan batun ba.
Kuma jaridar Punch ta ruwaito cewa, duk Kokarin da tayi na zantawa da kakakin majalisar abun ya ci tura, saboda an kasa samun lambobin wayarsa.
managarciya