2023: Dan Kudu bai kamata ya gadi Buhari ba------Tsohon Gwamnan Nasarawa

Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya gaya wa wadanda ke kira a mika shugabanci zuwa yankin kudancin ƙasar a 2023 da su binne tunaninsu zai fi masu kyau.

 Jaridar daily trust ta rahoto cewa Adamu wanda shi ne sanata mai wakiltar yankin Nasarawa ta yamma a majalisar tarayya ya bayyana mulkin karba-karba a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin Nijeriya.

 Duba wannan: APC ta tsayar da ranar zaben shugabanninta a jihohi

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba ya ce duk da cewa akwai kiraye-kirayen da ake yi na mika kujarer shugaban kasa ga shiyyar kudu maso gabas, amma babu wani tanadi na tsarin mulki kan hakan.

A cewarsa, tunda ra'ayin karba-karba ba ya cikin kundin tsarin mulkin kasar, kowane dan Najeriya da ya cancanta yana da 'yancin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba tare da la’akari da jiharsa ta asali ba.

Ya ce ba wata hujjar yanki, kana iya tura zuciyarka wani yanki da kanka ba dole sai an kai kujerar a can ba.