Mataimakin Kakakin Majalisar Kebbi, Ya Halarci Taron Yaƙin Neman Zaɓen Ƙananan Hukumomi 21

Mataimakin Kakakin Majalisar Kebbi, Ya Halarci Taron Yaƙin Neman Zaɓen Ƙananan Hukumomi 21

Daga Abbakar Aleeyu Anache, 

Dan majalisar jihar kebbi, mai wakiltar karamar hukumar mulki ta Zuru, a karkashin tutar jam'iyyar APC, Hon Usman Mohammed Ankwe, ya halarci taron kaddamar, da yan takarar Shugabancin kananan hukumomi, 21, a fadin jihar kebbi, 

Jam'iyyar APC, mai mulki a jihar kebbi a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku, Bagudu, ta kaddamar da yakin neman zaben kananan hukumomi 21, a garin Kamba, 

Hon Usman Mohammed Ankwe, yana daya acikin wayanda suka halarci taron kaddamar da Chiyamomi, a fadin jihar kebbi,

Hon Usman Mohammed Ankwe Zuru, ya nuna gamsuwa dangane da yadda al'umma suka zabe jajirtatun shuwagabanni domin basu damar jagorancin su, a kananan hukumomi 21, kuma ya yabawa uwar jam'iyyar APC, ta jihar kebbi 

Ankwe ya yabawa jam'iyyar APC ta kasa da kuma ta jihar kebbi, a karkashin jagorancin Abubakar Kana Zuru, ta yadda aka gudanar da wannan babban taron acikin lumana, 

A cewar Hon Usman Mohammed Ankwe, Zuru tare da duk sauran yan majalisun jihar kebbi suna nuna, gamsuwa dangane da yadda aka gudanar da wannan taron yakin neman zaben, na kananan hukumomi 21, dake fadin jihar kebbi,

Wannan taron da ya gudana acikin garin Kamba, ya kumshi al'umma da dama da kuma shuwagabannin al'umma, irin zaratan al'umma da aka zabo acikin wannan tafiyar ke, nuna nasara fili domin kuwa duk cikin wanda aka baiwa jagoranci acikin wa'dannan al'umma, babu wanda ba jajirtacce bane, babu wanda baida mutunci,

Hon Usman Mohammed Ankwe, Zuru ya bayyana cewa matakin da jam'iyyar APC, ta dauka yana nuni ne abisa kyakyawar shugabanci mai inganci na, gwamnan jihar kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, 

Ankwe ya jawo hankalin shuwagabannin da aka tsayar yakin neman zabe da suyi koyi da shuwagabanni nagari, kuma su jajirtacce domin ciyar da al'umma gaba, ya kara da cewa ya zama wajibi da yan takarar da aka tsayar suyi matukar faran tawa jam'iyyar APC, a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu,