APC Ta Kwace Kujerar Gwamna Hannun PDP a  Sakkwato

APC Ta Kwace Kujerar Gwamna Hannun PDP a  Sakkwato

 

Jami'in tattara sakamakon zabe a jihar Sakkwato Farfesa Armiya'u Hamisu ya bayyana dan takarar jam'iyar APC Alhaji Ahmad Aliyu Sokoto ne samu nasarar lashe zaben da aka yi a ranar Assabar data gabata.

Farfesa ya sanar APC ta samu kuri'a 453,661 in da ta doke jam'iyar PDP da dan takararta Malam Sa'idu Umar Ubandoma in da ya samu kuri'a 404,632.
Farfesa wanda yake shugaban jami'ar Dutsinma ya ce Ahmad Aliyu ya cika sharuddan da aka gidanya na dokokin zaɓe kan haka ya samu yawan kuri'un da aka kada don haka shi ne ya yi nasara.
Haka ke nuna a karshe dai jam'iyar APC ta kwace kujerar Gwamna daga hannun PDP a jihar Sakkwato.