Babbar kotun tarayya dake zamanta a Gusau, jihar Zamfara, a ranar Talata ta soke zaben fidda gwanin dan takaran gwamnan jihar karkashin jam’iyyar PDP.
Wannan ya biyo bayan soke zaben farko da kotun tayi a watan Satumba.
Dauda Lawal-Dare ne ya lashe duka zabukan biyu.
Alkalin kotun yanzu ya bayyana cewa gaba daya jam’iyyar PDP ba zata gabatar da dan takara a zaben gwamnan jihar ba da za’a gudana a 2023, rahoton ChannelsTV.
Zaku tuna cewa a watan Satumba, kotun ta soke zaben fidda gwanin farko sakamakon karar da Ibrahim Shehu da wasu ‘yan takara suka shigar.
Kotun ta yi umurnin a gudanar da sabon zabe kuma Lawal-Dare ya sake lashewa.
A riwayar TVC, hukuncin kotun ba dan takaran gwamnan kadai ya shafa ba, abin ya game da dukka sauran yan takara wata kujera a jihar.





