Mun Kashe Tiriliyan N3.2 Da Muka Kwato Daga Barayin Gwamnati — Abubakar Malami

Mun Kashe Tiriliyan N3.2 Da Muka Kwato Daga Barayin Gwamnati — Abubakar Malami

Ministan Shari'a babban Lauyan gwamnati Abubakar Malami, yace Najeriya ta kwato Naira triliyan 3.2 da aka sace daga kasar aka boye a bankuna daban-daban a duniya.

Rahoton Aminiya Abubakar Malami ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da yan jarida a Fadar shugaban kasa a ranar Alhamis 
Ministan yace Ma’aikatarsa ce ta jagoranci kwato makudan kudaden daga shari’o’I a kasashen duniya a tsakanin watan Maris na shekara 2021 da watan Mayu na shekara 2022.
Malami, ya ce anyi amfani duka kudin akan ayyukan raya kasa a wurare daban-daban a fadin kasar nan, wanda suka hada da ginin gadar 2nd Niger, aikin titin Abuja zuwa jihar Kano, da kuma aikin titin Legas zuwa jihar Ibadan. 
Ministan shari’a ya ci gaba da cewa, Gwamnatin ta samu Naira biliyan 1.82 daga sayar da takardun lamuni da kuma sayar da wasu kadarorin ta da aka kwato daga hannun barayin gwamnati.