GOSHI: Fita Ta Uku

GOSHI: Fita Ta Uku

GOSHI

_*MALLAKAR*_
_*Umma Yakubu Imam(Maman Dr)*_


P-3

A daddafe Bilkisu ta iya miƙewa tsayi, ya yin da ta nufi gidansu cikin kuka da majina shaɓe-shaɓe a fuskarta wacce goshinta ya yi mugun tsini har wani ƙyalli yake fitarwa tamkar an mulka mata man ƙuli-ƙuli, leɓan bakinta kuwa tuni ya tashi kamar an kwaɓa fulawa da yis. Ko da mahaifiyar Bilkisu ta yi ido huɗu da fuskar ƴarta a kumbure, ta wani zabura tsaye daga zaunen da take. Tambayar Bilkisu ta shiga yi da cewa, "Na shiga uku, waye bugeki da mota? Ko me babur ne ya kaɗe ki haka har ya canja miki kamanni Bilkisu? Wadda tun daga farko Bilkisu ta fara zayyano abin da ya haɗasu da goshi a makaranta tiryen-tiryen har kawo yanzu da ta tare ta akwanar gida ta yi mata mugun duka cikin wata iriyar murya mara daɗin amo saboda kumburin da bakinta ya yi. Mahaifiyar Bilkisu ce ta zari hijabi cikin sauri ta tasa ƙeyar Bilkisu a gaba suka nufi makaranta rai a matuƙar ɓace tana sababi.
Shigarsu makarantar ke da wuya suka iske kowa ya tafi sai malam Bukar da hidimasta da suka saura suna tattaunawa akan litattafan da gwamnati ta kawo kyauta a rabawa ɗalibai. Da ƙayar malam Bukar ya shaida Bilkisu domin komai na fuskarta sai da ya canja musamman baki da goshinta. Malam Bukar da ya ji Goshi ce ta aikata wannan aika-aikar ya ce, "Amma yarinyar nan goshi ta cika tantiriya, za kuma ta ɗan-ɗana kuɗarta a hannuna daidai gwargwadon abin da ta yi, duk gargaɗin da na yi mata ashe ba ta ji ba? Wai ma da me ta bugeki ne Bilkisu?

"Da hannu ta ce mini ta bugeta tamkar ta samu jaka, wallahi ba zan taɓa yarda a ci zalin ƴata ina da rai a doron duniya ba, tilas a bi mata haƙƙinta a kuma Sanya hukuma aciki kafin a kai ga zuwa gidan su yarinyar nan." Cewar Mahaifiyar Bilkisu da ke tsaye hannunta na saman kan Bilkisu tana sake jujjuyawa Hidimasta da malam Bukar da suka shiga baiwa mahaifiyar Bilkisu haƙuri duba ga an sallami dukkan ɗalibai duk sun tafi gida bare a samu Wanda zai raka su gidan su goshe, tun da ita Bilkisu ta ce ba ta san gidansu ba, suma kuma haka ba wanda ya san gidan. Da ƙayar da siɗin goshi Mahaifiyar Bilkisu ta haƙura zuwa gobe a je gidansu Goshi asamu iyayenta asan abin da za a yi, bayan tarkato maganin rage zugi da zazzaɓi da suka tulawa Mahaifiyar Bilkisu a baiwa Bilkisu saboda kumburin fuskarta da kuma tsamun jiki na bugun da tasha a hanun Goshi.


****


"Ɗan maliyo maliyo!

"Maliyo...

"Ɗan maliyo nawa!

"Maliyo... 

"Ya tafi Ina ne? 

"Maliyo... 

Da ga Maliyon da Goshi ta shigo da shi a baki ba sake cewa komai ba, ta tsuke bakinta tare da tsayawa a tsakar gida tamkar ba ita ba, idanuwanta da suka yi dirar mikiya kan tarin jama'ar da ba ta yi tsammanin ganin su a wannan lokacin ba kowa kuwa ya zubo mata ido ban da Ummanta da ke sharɓar kuka tamkar wacce aka aikowa da saƙon mutuwa.
Saɗaf-saɗaf Goshi ta zo za ta wucce ke nan ɗan wan Baffa da ke gefan Adda Hauwa ya doka mata wata uwar tsawar da ta tsaya tsam daga inda ƙafafuwanta suka dira.  Cikin sulo ɗin murya ɗan wan Baffan ke cewa, "Ga baƙar munafukar nan ta dawo adda. 

"Au ni ce baƙar munafuka? Goshi ta furta tana mai nuna kan ta da ɗan yatsan hannunta na kusa da babban. Ɗan wan Baff da ya kira ta da baƙara munafuka ya ce
 "I, ke ce ko za ki sakan na jakai ne? A fusace goshi ta kuma cewa, "To wai ma Awilo a ina na yi maka baƙin munafuncin da za ka ce mini baƙin munafuki algungumi ?

Faka-faka Awilo ya fara laluban madokin da zai doke Goshi. Adda Hauwa ta ce, "A hir ɗin ka Awilo kar ka kuskura ka taɓan jika wallahi ranka zai mummunan ɓaci. Cike da fushin da ya bayyana a fuskar Awilo ya jefar da tsintsiyar da ya rarimo yana mai cewa,

"Darr! Daman ni na San za a rina, an saci zanin mahaukaciya, wallahi Adda ke kike goyawa munafukar yarinyar nan baya take shatata rashin mutuncinta yadda take so. Yo ban da iskanci irin na Goshi a ina ƴa ta taɓa nemowa uwarta Kishiyar ma da ta tashi nemota sai ta nemowa uwarta shirgegiya me zubin Bauna? "Amma dai ba uwarka ta nemowa ba ko? Kuma Kar ka kuma iskantamun jika saboda ta yi aikin da babba me hankali yakamata ya yi don samun ladan haɗa sunnar manzon Allah S'W'A'. Cewar Adda Hauwa a fusace Awilo ya cafke zan cen da cewa'

"Oho! Ai uwattace ba uwata ba Adda ja ta ta cigaba da iya shegenta ni dai duk ranar da yarinyar nan ta shigo gonata na rantse da rabbis samawati wal'ard sai dai ki tsinceta ɗai-ɗai-da-ɗai-ɗai na rabata gida bakwai. "Ka raba ta gida goma ma Kar ka saurara mata don ubanka aure kuma Goshi ta haɗa shi da ƙarfin ikon Allah sai an ɗaura maƙiya su ji kunya. 
Takaici da baƙinciki ne ya sa Awilo sakin wani jahilin kuka, ya yin da ya yi waje da burgujejiyar rigarsa da bujen wandonsa, ƙarafunan wayensa sai kacakar-kacakar suke tamkar wani bajimin Kare. 

Adda Hauwa ce ta miƙe tsaye tare da kamo hannun Goshi ta zaunar da ita a kusa da ita. Baffa, Umman Goshi da yayarta Na'ima duk suna zaune Adda Hauwa ta buɗe baki cikin sanyin murya da cewa, "Ina takwarata ɗiyar albarka irin arziƙi take? 

"Gani nan a kusa da ke Adda ta. Goshi ta furta, cike da murmushi Adda Hauwa ta ɗora da cewa,

"Yawwa! Goshina faɗa mini gaskiyar lamarin nan kin ji, tsakaninki da Allah wai ke kike zuwa gidan Inna Sahura ki na cewa Baffanki na gaisheta ita da Uwani? Kin ga har gida Inna Sahura ta zo game da zan cen Baffanki da kuma uwani haka ne ko ba haka ba ne ɗiyar albarka? Goshi ta yi shiru kafin ta ce, "To tsakani na da Allah dai zan faɗi gaskiyata har cikin zuciyata Adda saboda mai ƙarya an ce ɗan wuta-bal-bal ne duk ƙawayena an yi musu Anti ni kaɗai ce kawai ban da ita. Kuma wallahi Adda ba ki ga yadda Antinansu ke lallaɓasu da basu abin duniya ba ni kuwa ko kallona Umma ba ta yi ballantana ma ta lallaɓani Adda ya Na'ima kaɗai take kulawa acikin gidan nan na rasa me na yi wa umma. Raurau idanun Goshi ya yi kamar za ta saki kuka Adda Hauwa ta ce, "Duk na ji wannan Goshi ba kuma laifinki ba ne na san nawa ne da na saka Baffa ya raɗa miki sunana, tambayar da na yi miki ke kike zuwa gidan Inna Sahura ko ba ke ba ce?
"Ni ce nana da ƙafafuwana Adda saboda Baffa ya auro mana Uwani tifar yashi...A fusace Umman Goshi da ke zaune a gefe ta miƙe haɗe da cacimo wuyan Goshi ta fara narka cikin kuka da ƙaraji. Adda Hauwa ta yi kan ta don ƙwatar Goshi daga hannunta. Kiciniya sosai Adda da mahaifiyar Goshi suka fara yi. Adda Hauwa na ƙoƙarin ƙwace Goshi daga hannun Ummanta, Ummanta na kaiwa Goshi duka Baffa da ke gefe a zaune na yi wa Umman Goshi magana ta saki Goshi tun da Adda ta ce ta bar bugunta haka amma taƙi ji sai ma maganganu da ta shiga yi marasa daɗi tana cewa,
"Ai daman ni na san ba ƙaunata kike yi ba Adda saboda ban ga dalilin da zai sa a yi mini Kishiya haka kawai batare da laifin tsaye ko na zaune ba. Me na yi miki Adda? Me na tsare miki ko ni zan baiwa kaina haihuwar Ɗa namiji, wallahi tallahi sai na karairaya yarinyar nan a gidan nan tun da ni na haifota ba ita ta haife ni ba. 
Kuka sosai Adda Hauwa ta rushe da shi tana cewa" Innalillahi wa inna ilaihir raju'una. la'ilaha'ilallahu Amina ni kike zagi a gabana kike gasan magana haka? Ni fa uwar mijinki ce ba sa'arki ba tun da na ce a sakawa yarinyar nan Goshi sunana kika ɗora mata karan tsana saboda mugun hali irin naki to wallahi Allah ya fi dubunki abin da kika yi min na sharrin haihuwar Ɗa namiji kuma na barki da Allah Amina. Baffa da tuni idanuwansa suka kaɗa suka yi jajir tsabar tashin hankalin ganin hawayen da Adda ke zubarwa. Ba zato bare tsammani Baffa ya wankawa Umman Goshi zazzafan mari, Wanda ya sa ta zauna daram a ƙasa yana cewa, "Ko ki so ko kar ki so aure kamar na yi shi na gama da Uwani Amina ban san bakida mutunci ba sai yau, mahaifiyartawa kike gayawa baƙaƙen maganganu? Tuni Goshi ta Yi bayan Adda Hauwa ta ɓuya. Adda Hauwa ta zura takalminta rai a matuƙar ɓace mayafin ma aka ta ɗorashi tare da janyo hannun Goshi suka yo waje, shi ma Baffa ya biyo bayansu. Umman Goshi kuwa da ke zaune daɓar a ƙasa na kuka wiwi yayar Goshi Na'ima na bata haƙuri cikin kuka ita ma.

@Real Maman Dr@
(2025)