WATA UNGUWA: Fita Ta 14

WATA UNGUWA: Fita Ta 14

BABI NA SHA HUƊU

 

 

Da wannan tunanin Fa'ee ta rarumo wani guntun ice wanda ake kira bakin wuta, ta yi kan Atika.

Sai da ta ware iya ƙarfinta ta laftawa Atikar shi a gadon baya.

Sai dai da alama matar bata ma san tana yi ba don ji ta yi tamkar susa ce Fa'een ta mata.

 

Lura da hakan ya ƙara tunzura budurwar ta juya baya da sauri tana waige-waige, can idonta ya yi tozali da wani madai-daicin dutse.

 

Cikin azama ta nufi gun tare da sanya duka ƙarfinta ta tallabi dutsen ta nufi gurin da Atika ke zaune kan ruwan cikin Mamanta.

 

Ba tare da tunanin komai ba, ta ɗaga shi tare da kwabɗawa Atika shi a tsakar ka da iya ƙarfinta.

 

"Ah wayyo! Wayyo Allah!" Atika ta saki wata irin razananniyar ƙara.

A gigice ta saki wuyan Maman Fa'ee da take damƙe da shi ta saka hannun akai ta shafa.

 

A razane ta dawo da hannun saitin fuskarta tana kallon jinin da ta shafo daga kanta, lokaci ɗaya kuma tana jin raɗaɗin raunin dake kan nata.

Lokaci ɗaya ta dakatar da mamakin da take, ta gayyato mummunan ƙuduri zuwa zuciyarta.

 

Cikin baƙin nufi ta nufi Fa'ee ta janyo ta ta haɗa su guri ɗaya da Mamanta da ta yi nasarar miƙewa daƙyar, ta gwara kansu guri ɗaya.

 

Dukkanninsu suka saka ƙara a tare, a dai-dai lokacin da ita ma Atikan jiri ya fara ɗibarta, kasancewar sosai kanta ya fashe sai ambaliyar jini yake.

 

Bata da zabin da ya wuce ta ta sake su, tare da komawa gefe ta faɗi zaune rikicaa.

 

Ganin hakan ya saka a rikice tsamurarren mijinta ya je ya tallafo ta suka nufi waje.

 

Sauƙinta ma gidan nasu kusa da titi ne sosai, duk da sun shiga lungu, hakan yasa ba su sha wahala ba gurin samun Napep.

A nan suka nufi asibiti mafi kusa.

 

"Allah ya miki albarka Fa'ee! Duk da dai ban so kin saka kanki a wannan rigimar ba." Maman Fa'ee ta faɗa tana kallon 'yar tata.

 

Murmushin ƙarfin hali Fa'ee ta yi ta ce "kada ki damu Mamana, ni ai bana tsoron rigima komai girmanta. Ba ma yanda za'ayi na zuba ido ina kallo a cutar mun dake."

 

Ta ji daɗin kalaman 'yar tata sosai don haka ta kuma saka mata albarka tare da janta suka wuce ɗaki don su huce gajiyar da Atika ta tara masu.

 

Sai a lokacin ne kuma 'yan kallon faɗan suka watse, kowa ya ci gaba da sabgar gabansa. Shamsiyya da Sakina da ta shigo gidan ɗazu don siyen Abinci da Matar Garbe Kanuri ke siyarwa, ta tarar ana rigimar ta tsaya kallo suka ci gaba da tofa albarkacin bakinsu.

 

Shamsiyya ta kalli Sakina ta ce "Uhmm! Ke ai mu a gidan nan muna shan kallo, kuma mun tara kalolin mutane harda bara gurbi. Ko da yake renon marasa tarbiyya ai ba za a tsammaci ya yi ladabi ba balle kuma biyayya ga na gaba."

 

"Hmm! Ke dai bari Shamsiyya na so ace nan gidan nake, da kullum zan samu sababbin rahoto a bati ba sai na nemo ba. Allah ya shirya inda rabon shiryuwar, amma kam Allah ya wadaran reno irin wannan." Ta faɗa cikin yanayi na taya ƙawarta neman rigima.

 

Duk abubuwan da suke faɗa a kan kunnen Fa'ee, domin a saitin ƙofarsu Fa'een suke zaune.

 

Sai dai a karon farko ta yi masu damo kamar bata ji ba.

 

 

Shamsiyya da neman rigima da ta ga haƙarta bata cimma ruwa ba, sai ta sake jarrabawa a karo na biyu.

 

Riƙe haɓa ta yi ta ce "To! Wannan addu'ar taki sai dai ace ameen kawai, amma abun da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Su O'O an yi asarar hali wallahi."

 

Dariya Sakina ta saka, itama Shamsiyyan ta taya ta sai ƙyaƙyatawa suke.

 

Nan fa Fa'ee ta cika fam, miƙewa ta yi da nufin ta je ta kacalcala mutuncinsu. Sai mamanta ta dakatar da ita ta hanyar riƙe hannunta ta girgiza mata kai alamun A'a.

 

Sai dai ta riga ta zo iya wuya ta yanda ba ta jin akwai wani abu da zai iya dakatar da ita. Don haka ta fisge hannun daga riƙon da Maman Tata ta mata ta yi kansu gadan-gadan.

 

"Ku marasa mutunci! Har kun isa ku zauna a ƙofar fadata kuma ku zage ni? Kuna tunanin zan ƙyale ku ne?" Ta faɗa cikin ɗaga murya.

 

Basu ce mata ƙala ba sai kallonta da suka yi tare da bushewa da dariya.

 

Kukan kura ta yi tayo cikinsu, ta kuwa yi sa'ar damkar wuyan Sakina ta miƙar da ita tare da shaƙe ta sosai. Cikin zafin rai take jujjuya idanunta da suka ƙara girma ta ce "Ke kuma jikar ɗan ubayyu me ya sanyo bakinki a cikin sabgar gidanmu? Me ma kika ce? Ki ka ce Allah ya wadaran reno irin wannan ko?"

 

Gyara tsayuwarta ta yi ta ƙara da cewa "Ba gwanda irin wannan renon ba da irin renon da kika samu? Munafunci da zugudidi duk ya ƙare a danginku, kifaye kawai masu cinye junansu."

 

Tuni idon Sakina ya raina fata don ba ta da ƙarfi sai kaifin baki, ga ta siririya kamar iska zai ɗauke ta. Sai wuƙi-wuƙi take da ido ta rasa mai cetonta.

 

Shamsiyya ce ta miƙe ta yo kan Fa'een da nufin tarewa ƙawarta faɗan, nan fa Fa'ee ta fara fella mata lafiyayyen mari da ɗaya hannunta kafin ta juyo ta ɗauke Sakina da kyakkyawan Mari sannan ta ingiza ta baya ta na faɗar "Ke idan na ce zan yi faɗa da ke ma ba abunda zan tsinta don namanki ya mun kaɗan, me zan tsinta a wannan ƙashi, fice mana daga gida."

Ta karashe zancen da bada umurni.

 

Cikin hanzari Sakina ta bar gidan ganin zata sha wuya a karon banza da wofi.

 

A nan ne kuma faɗan ya koma tsakanin Shamsiyya da Fa'ee dama ko waccensu jiraye take da ɗayar, mussamman Shamsiyya da ta kasa manta abunda Fa'een ta mata a jiya.

 

Sun ɗauki mintuna suna rigimar ba wanda ya tamka su, can sai ga Jilde bafulatana ta shigo gidan da sallamarta.

 

Ganin abunda yake faruwa ya sa ta nufi gun tana faɗar "Assha! Assha!! Kai don Allah mi nene haka kuna yi? Don Allah ku yi hakuri bai kamata kuna faɗa da zuna haka ba."

 

Jin hakan ya saka Fa'ee da tsaurin ido ya mata yawa ta juyo a hasale ta ce "Ke don Allah Malama matsa daga nan! Dube ki, wai kin zo sulhu, ina ma ruwanki da mu ne? Dama Fulanin dajin nan idan kuka shigo birni kun fi kowa fi'ili."

 

Sum-sum Jilde ta ja ƙafafunta da suka yi sanyi ta wuce ɗakinta tana matsar ƙwalla, duk da cewa kowa yasan Fulani da zuciya, amma ita Jilde bata son rigima ko kaɗan. Sai dai idan aka yi akasin baƙanta mata har ta yi zuciya to akwai matsala. To yau kan Fa'ee ta yi matuƙar ɓata mata rai tunda har ta yi ƙwalla.

 

 

Da misalin ƙarfe 6pm Fa'ee na zaune kan kujera a ƙofar ɗakinsu tana cin tuwo da miyar kuka ta jiyo jiniyar motar 'yansanda a waje.

 

Mamaki ne ya cika ta can ƙasa-kasa ta ce "yansanda kuma a layin nan? To me suka zo yi? Bari in yi sauri in ƙarasa don kada kallo ya bar ni ta sha."

 

Da sauri-sauri ta ci gaba da cin tuwon. Ga mamakinta sai ta ji kamar jiniyar a ƙofar gidansu ake.

 

Kafin ta kai lomar ƙarshe sai ga 'yansanda Uku sun shigo gidan biyu mata ɗayan namiji, da alama shi ne Ogansu.

 

"Wacece Fa'iza a gidan nan?"

Ogan Ya tambaya cikin murtuƙe fuska.

 

Nan take tsoro ya ziyarci Fa'ee ƙirjinta sai bugawa ya ke. Kafin ta buɗi baki ta ce wani abu ya daka tsawa a karo na biyu yana maimaita tambayarsa.

 

Shamsiyya da ta fito banɗaki yanzu ta nuna Fa'ee da yatsa ta ce "Gata can."

 

Nan suka nufi gunta ita kuma ta soma ja da baya, tamkar mara gaskiya tana kiran Mamanta. Ankwa suka saka mata a hannu tare da ingiza ƙeyarta zuwa waje.

 

Mamanta sai ihu ta ke tana faɗar "Ku sake mun 'yata? Me ta muku ina za ku kaita.?"

 

 

To fah! Jama'a Fa'ee a hannun kwalawa ko ya zata kaya?

 

Laifin me ta yi aka kamata?

 

Ya labarin Atika da mijinta anyah zasu haƙura da wannan aika-aikar da Fa'ee ta masu?

 

 

Ku dai ku ci gaba da biyo alƙamin Ummu inteesar don jin ya zata kaya.