MAGEN KULU: Labarain Hikaya Fita Ta 3

MAGEN KULU: Labarain Hikaya Fita Ta 3

MAGEN KULU

 

               Na

Hauwa'u Salisu (Haupha)

 

Lokacin da Sarki Yakubu ya ga wannan Mage sai  ya tuna da wani tsohon mafarkinsa wanda a lokacin da ya yi mafarkin yana tsaka da neman haihuwa ne ruwa a jallo.

 

Bai ɓata lokaci ba ya aika aka kira masa Bokan dake aiki a masarautar ya gaya ma shi abin da ke faruwa.

 

"Ina cikin ɗaki zaune tare da wani gudan jini babba wanda jinin tamkar an tace shi saboda kyansa sai ga wata Mage ta bayyana cikin ɗakin burinta shi ne ta cinye wannan gudan jini ni kuma na hanata mu kai ta faɗa da ita sosai wanda daga ƙarshe ta yakushe ni ta ɓace bat, lokacin da zan dubi inda gudan jinin yake sai naga ya narke yana bin ƙasa tana tsotse shi."

 

Bokan ya ƙurawa Sarki Yakubu ido kafin ya kwance jakarsa ta tsubbu ya fara sulkullensa. Bai ɗauki lokaci mai tsawo ba ya dakata yana goge zufa, tabbas ko kare ke cizonsa bai isa ya bayyana abin da mafarkin Sarki ke nufi ba, amma ina mafita ?

 

Sarki Yakubu ya dakawa Bokan tsawa mai razanarwa "Ban kira ka don ka dinga goge zufa ba, sai don ka warware min matsalata ka bayyana min abin da mafarkina ya ƙunsa."

 

Cikin dakewa Bokan ya rusuna ya nemi afuwa ya ce, "Allah Ya huci zuciyarka ya baka tsawon kwana, haƙiƙa wannan gudan jinin ɗanka ne da zaka haifa, ita kuwa Magen nan wata yarinya ce da zai gamu da ita mai tarin baiwa da abubuwan al'ajabi sai dai talaka ce kuma marainiya ce wadda bata da cin yau balle na gode asalima zata kasance mai dakon bakin hanya don neman abin da zata ci... Bai kai ƙarshen maganarba Sarki Yakubu ya kwashe bakinsa da mari sai da haƙora biyu su kai fitar burgu ya dubi bokan yana huci ya ce, "Na rantse da ƙarfin mulkina babu wata matsiyaciyar da zata shigo cikin zuri'ata in dai ina da numfashi."

 

Bokan ya dube shi zuwa yanzu yasan komai zai iya faruwa ya ce, "Idan kai kasadar raba ɗanka da yarinyar tabbas zai mutu wanda hakan zai sa ka jawo bala'i da zai dinga bibiyar garin nan na har abada... Sarki ya amshe a fusace "Idan kana raye kenan zaka tabbatar da faruwar hakan ai ko? Ya zare takobinsa ya fille kan Bokan ya tashi yana kaiwa da komowa. Ba ai wata ba aka samu cikin Yarima Muhammad, tun a bin na damunsa har ya manta to yau ga shi ya ga magen sak wadda ya gani a mafarkinsa fara sol mai ido kala biyu.

 

Cikin sauri Sarki Yakubu ya isa ɗakin Yarima abin mamaki ya iske yana zaune yana cin ƙosai, bayan kowa yasan kwance yake sai an kwantar an tayar .

 

Yarima na ganin mahaifinsa ya fashe da kuka yana ambatar sunan Hauwa mai ƙosai abin gwanin ban tausayi.

Idan ran Sarki ya yi dubu to ya ɓaci don haka ya fice rai ɓace bai tanka ma Yarima ba.

 

Ko da ya fice yasa aka kira ma shi Shafi'u mai rake, sun jima suna magana sannan Shafi'u mai rake ya fice yana murmushi.

 

Hauwa na kwance ita da Magenta sai ji ta yi an warce mata Mage, Shafi'u ne tsaye da Magen ya shaƙe mata wuya yana kallon Hauwa yana dariyar mugunta.

"Yau dai ko tare ku ka zo duniya ke da Magen nan to yau zan raba ku Hauwa, tabbas yau Magenki zata mutu Hauwa!

 

Bai saurari magiyar da Hauwa ke yi ba, ya fice da Magen Yana jin daɗi, kai tsaye daji ya nufa, sai da yayi tafiya mai nisan gaske ya tabbatar da yayi nisan gaske sannan ya dubi wata ƙatuwar bishiyar Tsamiya ya buga Magen jikinta ya juya yayi tafiyarsa.

 

Sai dai kamar wasa ya kasa gane hanyar komawa gida, ya yi yawo sosai har ya galabaita amma bai gane hanyar komawa gida ba ga dare yayi yunwa da ƙishirwa duk sun addabe shi, takalminsa ya tsinke bala'i nan da nan ya same shi.

 

Dole Shafi'u ya saduda dare yayi sosai don haka ya nemi wajen kwanciya ƙasan wata bishiyar Kanya ya kwanta yana maida numfashi.

Sai dai nan take kukan Mage ya cika dajin marar daɗin ji, har wani jan sunansa take a kukan nata. Nan da nan tsoro ya kama shi, ya fara kyarma kamar tsohon da ya kwana biyu a duniya.

A takaice dai haka aka dinga tsorata Shafi'u a dajin nan har gari ya waye, babu irin ihu da rakin da bai yi ba amma na banza don babu mai jinsa.

 

Sai da gari ya waye sannan ya gane hanya, ya dawo gida hajaran-majaran sai dai yana shiga cikin layin gidansu Hauwa ya hangota tana toya ƙosai ga Magenta a gefenta sai ɗaga wutsiya take tana halbin iska da bindinta.

 

Hauwa ko kallonsa batai ba tuyar ƙosanta kawai take ba ji ba gani. Magen ya kalla sai ya ga shi kawai take kallo kamar zatai ma shi magana.

Cikin gida ya wuce mutane nata kallonsa kamar wani mahaukaci.

 

Hauwa na gama saida ƙosan ta dawo gida ya fara tambayarta ta ina Magen ta dawo ?

 

Hauwa ta ce "kana fita ba da jimawa ba na ganta da gudu Ni dai."

Tsaki ya ja "Shegiya mayyar banza ni ina can na ɓace saboda ita ashe ita ta jima da dawowa gida ma, to wallahi Hauwa na gaji da Magenki ki san yadda za ki da ita ba zan ci gaba da zama da ita ba ni."

 

Hauwa idonta ya ciko da hawaye ta fara ba shi haƙuri amma kamar tana ƙara zuga shi, haka Hauwa ta yini kuka a ranar.

 

Yarima Muhammad kuwa sai ciwo ke gaba, abin da ya ɗaga hankalin Sarki Yakubu kenan har ya fara tunanin inda zai kai Yarima Muhammad ai ma shi magani.

Sai dai duk inda ya kai shi amsa ɗaya ce a barshi ya auri Hauwa shi kam Sarki idan akwai sunan da ya tsana bai wuce Hauwa ba.

 

Daga ƙarshe Yarima ya amsa kiran mahaliccinsa abin da ya harzuƙa Sarki Yakubu kenan ya fara neman hanyar da zai kashe Hauwa ya ɗauki fansar ɗansa.

 

Cikin lokaci kaɗan ya sa Shafi'u ya amshi dodon maita wanda ya dinga yin suffar Magen Hauwa yana shiga gidajen mutane da dare yana basu tsoro.

 

Nan da nan mutane suka fara maganar ashe da gaske Hauwa mai ƙosai mayya ce kowa ya ce ya ganta gidansa da dare.

 

Sai aka daina siyen ƙosan Hauwa mutane suka daina kulata kowa ya ganta sai ya ruga nan da nan Hauwa ta zama abar ƙyama a garin.

 

Ba'a saida mata abu itama ba'a siye gunta sai dai duk da haka kullum sai ta fito ta toya ƙosan ta zubama Magenta kaskon farko sauran kuwa ba wanda yasan yadda take da shi.

 

Hauwa na cikin wannan kyara da tsangwama ta mutanen gari sai annobar fari ta sauka a garin waɗanda duk in suka sauka kan mutum sai wasu manyan ƙuraje su bayyana a jikin mutum suita zugi kwana biyu kacal sai tsutsoci su fara zubowa daga cikin ƙurjin.

Babu irin masu maganin da ba'a kira ba amma an kasa maganin wannan annobar.

 

Sai da ya kasance mutane sun ɓoye a ɗaki ba mai fita ko tsakar gida gudun kada farin su taɓa mutum.

 

Sai dai abin mamaki Hauwa na yawo kuma bata fasa toya ƙosanta ba amma ba farar da ta taɓa hawa jikinta.

 

Wata rana ta zo wucewa da iccenta na toya ƙosai ta ga wasu yara nata kuka tsutsa na fita daga ƙurajensu ta aje iccen ta dubi Magenta ta ce, "Ki taimake su MAGEN HAUWA."

 

Sai kawai Magen ta isa gaban yaran ta dinga lasar duk inda ke da ƙurajen suna ɓacewa.

 

Nan take yaran suka warke su ka ruga gidajensu suna murna suka gayawa iyayensu.

 

Sai labari ya kewaye gari nan da nan gidan Hauwa ya cika da masu ciwon suna neman alfarmar ta saka Magenta ta lashe masu ƙurajen.

 

Hauwa baiwar Allah haka ta saka Magenta ta lashe ƙurajen tas kowa ya warke ta saka Magen ta dinga kama farin tana cinyewa har garin ya samu lafiya.

 

Babu abin da sarki bai sani ba don haka ya kira Shafi'u ya sake ba shi wani aikin akan Hauwa da Magenta.

Sai mutane suka fara ɗan sakin jiki da Hauwa musamman da suka daina ganin Magenta da tsakar dare wanda Magen ce ta cinye dodon tsafin Shafi'u don haka mutane suka daina ganinta.

 

Kwatsam Hauwa ta kwanta rashin lafiya mai tsanani wanda mutane sai suka fara gudunta babu mai taimaka mata da komai sai Magenta ita ce kawai ke kulawa da ita.

Ta jima tana cikin halin jinyar babu wanda ke mata ko sannu duk faɗin garin.

 

Ba'a ankara ba sai wayar gari akai garin duk wata rijiya dake da ruwa ta ƙafe idan aka tono sabuwa babu ruwa sai ai ta rami amma ba ruwa.

Rijiyar gidan Hauwa mai ƙosai ce kawai bata ƙafe ba da ruwa cikinta sosai kuma basu canja kala ba kamar yadda sauran Rijiyoyin garin suka sauya kala ba.

 

Ba kunya mutane suka koma gidan Hauwa mai ƙosai da ɗibar ruwa dare da rana suna can kuma ikon Allah rijiyar bata alamar kafewa.

 

Sun jima a wannan halin har zuwa lokacin Hauwa kwance take ba lafiya amma babu mai kulawa da ita kowa ruwa yake ɗiba ya fice ko sannu bata haɗa su da Hauwa.

 

Kwatsam ! Sai itama rijiyar gidan Hauwa ta fara ja da baya abin da ya ɗaga hankalin mutane kenan suka fara tunanin mafita kan lamarin.

 

Sarki Yakubu ya bada sanarwar yana neman kowa da kowa a fadarsa, nan da nan mutane suka tafi daman suna gudun su yi magana ne su ja ma kansu don kowa yasan Sarki Yakubu bai da kirki bai tausayin talaka ko kaɗan.

 

Suna zuwa Shafi'u mai rake ya miƙe tsaye ya fara basu labarin HAUWA MAI ƘOSAI ce ke turo masu masifa da bala'i don mayya ce tsafi take da Magenta Shi ya gani da idonsa sadda take tsafin.

 

Sarki Yakubu da kansa ya ɗora da cewa ita ce ta lashe masa ɗa wato Yarima Muhammad da idonsa ya ganta cikin dare.

 

Sai mutane kowa ya fara kawo nashi jawabin wanda duk yawanci ƙarya ne.

 

Ƙarshe suka yanke shawarar kashe Hauwa da Magenta ko bala'i zai dakata da ɓullo ma su.

 

Duk mutanen garin suka isa gidan Hauwa mai ƙosai tana kwance ba lafiya haka su kai shawarar rufeta da magenta a cikin gidanta.

 

Ba tausayi ba komai haka suka rufe MAGEN HAUWA MAI ƘOSAI da ita kanta HAUWAI.

 

Bayan wasu kwanaki da rufe Hauwa da Magenta Shafi'u ya samu kanshi da mafarkai kala-kala wanda duk MAGEN HAUWA yake gani ba kyan gani, dole ya tara jama'ar gari ya bayyana ma su gaskiyar maganar Hauwa bata da laifin komai son zuciyar Sarki ne yasa suka kashe ta, sannan bala'i dake faruwa garin ɗan Bokan da Sarki ya kashe ne yake turoshi ba ruwan Hauwa."

 

Yana zuwa nan ya dakata ya ce, "Malam Bello ɗora daga inda na tsaya."

 

To fa !

 

Ashe haka akai?