LISSAFIN KADDARA: Labari Mai Razana Zuciya

LISSAFIN KADDARA: Labari Mai Razana Zuciya

LISSAFIN KADDARA


*Ibnatu Sulayman*
  

Not edited

*DEDICATED TO SHAMSIYYA USMAN MANGA*

P*1&2

Bahaushe yace "dare mahutar bawa" tabbas dare lokacine da galiban mutane suka daukeshi a matsayi lokacin hutawa amma ga mai wayo dare lokacine na neman yaddar Allah,dare lokaci ne da bawa yake neman lahirarsa ko kuma duniyarsa,sannan kuma dare lokaci ne na neman yaddar Allah sanin haka ne yasa ta mike cikin yanayi na soyewar ido da rashin jin kasala ko gajiyawa da rokon Ubangiji abunda ta saba rokonshi duk daren duniya tunda tayi wayo  haka mahaifiyarta ta koyar da su tashi cikin dare da mika kokon bararsu gareshi, fita tayi ta dauro alwala tazo ta gabatar da nafila raka'a biyu sai dai takan tsawaita tsayuwarta da kuma sujjadarta,bayan ta idar ta kuma dora da lazimi sannan ta gabatar ta karatun alkur'ani mai girma dai-dai gwargwado,hannu ta daga sama tana rokon Ubangiji tare da yi masa kirari da sunayensa tsarkaka guda dari ba daya tare da tawassali da duk wani aikinta na alkairi da tayi ta sigar bayyana roko "ya Allah ina rokonka cike da kaskantar da kai,ni ba kowa bace face baiwar da lissafin kaddara yake neman salwantar da lafiyata da rayuwarta,ya Allah kai ka sanya kaddarata ta zama tsastsaurar jarbawata Allah kasa nacinye jarabawar nan,ya Allah karka nunamun  lokacin da zan bijirewa kaddarata,kan lokacin ya cimmini Allah kasa nacimma sa'a,ya Allah ka bani dauriyar daukar kaddarata duk girmanta da kuma yawanta Allah kaine Allah...."kuka ne yaci karfinta tama rasa wacce irin addu'a zatayi taji dadi mai yasa kowa yake yaruwa cikin nutsuwa da farin ciki amma ita banda ita "Astagfirillah"ta fada a bayyane tana tashi da nade abun sallah tare da hayewa 'yar yaloluwar tabarmarta ta kwanta  tana addu'ar Allah yasa bacci ya dauketa,sai dai fa shi bacci barawo ne lokacin da kake dakonshi ba lokacin yake bayyana ba maimakon bacci ya dauketa sai kawai ta lula duniyar tunani wanda hakan dabi'ace ta kusan kowanne mutum,
"Babu komai a cikin rayuwarmu banda tarin kaddarori kala-kala daga wannan sai wannan daga mun samu sauki mun dinke wata to nan zamu sake samun sabuwar baraka, kaddara ta fara lissafinta ne tun daga kan mahaifiyata koma nace mahaifinta daganan ta gangaro zuwa garemu amma dukda haka kullum cikin godiya ga Allah muke da ya sanyawa zukatanmu tawassali, mahaifiyata 'yar asalin kasar nigar ce su biyu kawai iyayensu suka haifa itace karama sai yayanta da tun baifi 11years ba mahaifinsu ya turashi Nigeria karatun allo lokacin ko haihuwar ta ba'ayi ba, iyayenta sun raineta cikin gata amma duk da haka basu sangarta ta ba sun bata ilimi dai-dai gwargwado Arabic da kuma boko,bayan ta kammala degree ta a fannin lissafi ne yayi mata zance aure tun daga lokacin lissafin kaddara ya fara kwankwasa kofa dominshi a tsarin kakanmu yafi kaunar auren hadi domin kuwa tun tana karama ya bayar da ita wa Dan yayansa yayin da ita kuma mahaifiyamu a lokacin Allah ya jarbceta da son wani class mate nata da yazo karu Nigar daga Nigeria kakanmu baitashi sa ni ba sai da soyayya ta huda zuciyar diyarsa ta yadda rabuwa zatayi wuya,da yawan mutane sukan fifita zabinsu akan zabin Ubangiji sukan manta neman zabin alkairi yafi neman zabin zuciya,haka ta kasance da mahaifiyamu domin ta fifita zabinta akan zabin mahaifinta , mahaifiyarmu ta bijirewa fadar mahaifinta yayin da tayi kunnen uwar shegu da maganarsa haka ba dan yaso ba yanaji yana gani Yayansa yasa takawo wanda takeso din akayi komai aka gama sai dai shi yace ba ruwanshi Kuma mahaifiyarmu ta amince duk domin cikar muradinta sai dai abunda ta kasa ganewa wanda mahaifiyarta ta sha tunatar da ita shi shine wani  namiji ba Dan goyo bane dan kunama ne, anyi aure lafiya amarya da ango sun wuce Nigeria ba tare da dan rakiya ba bisa umarni Mahaifinta,sun tsara zamansu cikin aminci suna zaune cikin farin ciki da jindadi kowa na damuwa da damuwar Dan uwansa ta haka ne angonta ya mantar da ita duk wani bacin rai dake tsakaninta da mahaifinta,anan haka ciki ya bayyana kullum cikin riritawa da nuna madarar soyayya suke sai dai angon nata kullum batun shin guda daya ne akan cikin nata "Maryam Dan Allah karki haifamun mace domin kuwa ni bana kaunar wata 'ya mace a duniya bayan ke,ke kadai nake so kuma ke kadai ce macen da zata shigo duniyata taji dadi, Maryam ki tabbatar kin samamun magaji" wannan maganar ba karamin tada hankalin mahaifiyarmu tayi ba domin kuwa tayi-tayi ta ganar dashi ba ita take bayarwa ba Allah ne Kuma kowanne ya basu su karba suyi godiya amma ya gaza fahimtar hakan shi kawai burinshi ta haifar masa namiji ba shiri mahaifiyata ta koma ga Allah ta koma rokon alkairi game da abunda ke cikin ta sannan takan fadawa Allah ya bata da namiji domin cikar burin mijinta abin soyuwa a gareta,.

Kwala kiran sallah asubah da akayi daga masallatai mabanbanta ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da take,fita tayi ta dauro alwala duk da waccan din ba karyewa tayi ba raka'atanil figr ta gabatar sannan ta zauna  lazimi har aka shiga masallaci ta tashi tabi liman,suna idarwa ta koma ta kwanta bacci mai nauyi yayi gaba da ita,


Ameenatuh! Ameenatuh!!
a firgice ta tashi bakinta dauke da salati ganin hasken da gari yayi sosai yasa ta mike tsaye ba shiri hade da fadin" Umma shine baku tashe ni ba har gari yayi haske haka,nasan ma yau bazanyi wani abun arziki ba in ma an barni na shiga""to ya kikeso nayi miki Ameenatuh tun dazu nake kanki nake faman kwalla miki kira shiru,ki tashiyi wanka ga kununki can kisha ita dai  Khadija tayi gaba"da sauri ta dago tana kallon mahaifiyarta ta kafin cikin karyar da kai tace"haba Umma sa nin kanki ne Khadija bata da lafiya taya zaki barta ta fita aiki bayan duk wata matsala da take damunta sanadiyyar aikin qaron nanne""ni ma nace kartaje ta nace sai taje kuma naga jikin nata da dan sauki jiyafa kina gani tun fitowar rana har faduwarta ba abunda muka kai baki banda ruwa yanzu ma wancan kunun da nace kije kisha a gidan Alhaji Hamisu aka raba sadaka" tana gama maganar ta fice ta bar Ameenatuh a wurin tana faman jin radadin abin zuciyarta addu'a take Allah yasa bata makara sosai ba ko zasu hadu da khadija ta korota gida,


ko wanka bata tsaya yi ba tadaiyi brush tasha kunu sannan tayiwa Umma sallama ta wuce,tafe take tana addu'ar Allah yasa sugaban company baizo ba don batajin dadin haduwa da shi kwata-kwata,ba ta daina addu'ar ba har tashiga company sai dai addu'arta bata amsu ba domin har ya fito zagaye lokacin 9:07 gabanta ne yaci gaba da faduwa tana mai-maita kalmar innalillahi wa'inna ilaihirraji'un a fili domin kuwa ta tsanin ganin mutumin nan,sai da taje dab da shi sannan ta gaidashi cikin mutuntawa bai amsa ba dama kuma tayi tunanin hakan haka yasa tayi gaba abunta "ke!!!" a dan razane ta juyo tana kallonsa "karfe nawa yanzu da zaki shigomun company cike da gadara sai kace na ubanki!?" kawar da kai tayi kafin a hankali tace "yi hakuri dan Allah makara nayi ban tashi da wuri ba" wani banzan kallo ya watsa mata yana kara turo tunbinsa gaba tare da tabe mummunar fuskarsa yace"ok!! yayi kyau sosai ke har damar bacci kika samu  to ki koma gida daga yau aikinki ya juya dare in yaso sai kinayi baccin mai hujja da safe"ya karasa maganar yana kashe mata ido daya itakuwa marairaicewa tayi zata fara magiya ya juya abunsa ya shige ciki "Allah ya kiyaye ai ko zanrasa ci da sha wlh bazanyi aikin dare a wannan kazamin company ba" wanda takewa lakabi da matattarar shedan,


Da sallama tashiga gidan ta samu Umma zaune tsakar gida tayi tagumi "lafiya kuwa Umma?" a jiyar zuciya Umma ta sauke tana duban Ameenatuh tace"ina fa lafiya, Maman Aysha da take kawomana wankau yau naje zan karbo tace wai tayi sabuwar mai wanki namu baya fita,ga kuma naga alamun kema kamar ba lafiya ba ko maganar Khadija ce ta bata miki rai!?"zama tayi gefen Umma sannan tace "eh to da haka ma naso haduwa da ita ta dawo gida sai dai kan na kaiga shiga ya dakatar da ni wai  ya maidani aikin dare""innalillahi wa'inna ilaihirraji'un shikenan  mun rasa naki aikin da muke dan ko gurgura rayuwarmu dashi dan kuwa bazaki taba zuwa aikin dare wannan kazamin company ba na ranar ma rashin madafa ne,gashi yanzu Malam Sama'ila ya aiko wai kudin mu ya kare mutashi zai gyara gidansa amarya zaisa"kallon Umma tayi cikin yanayin da ita kanta ta kasa fassara wanne yanayi ta shiga  kan su gama  jimamin abunda ya samesu ne sukaji sallama gaba daya suka juya dan ganin masu shigowa, khadija ce ranga-ranga aka shigo da ita kamar wata gawa salati Umma tasa tayi kansu ita kuwa Ameenatuh tashin da zatayi sai jinta tayi akasa sumammiya tukan Umma ta karasa ga khadija tajuyo ga Ameenatuh wacce ta zube ba numfashi,kuka Umma tasa wanda ya dade yana cin zuciyarta tana furta "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!"

Kalmar da kawai take mai-maitawa kenan....