Bayan Shekara 42 Har yanzu yankin Sakkwato Bai samu Gwamna Kamar Shehu Kangiwa ba----Injiniya Aminu Ganda
Tsohon Gwamnan Sakkwato Alhaji Shehu Kangiwa ya yi gwamnan tsohuwar Sakkwato wadda aka cire jihohin Kebbi da Zamfara cikinta daga shekarar 1979 zuwa 1981 shi ne zababben gwaamna na farko tun bayan samar da jihar ya yi a jam’iyar NPN cikin jamhuriya ta biyu
Injiniya Aminu Ganda sanannen mutim ne da yake gwagwarmaya a harkokin mulki da siyasa a jihar Sakkwato wanda yake rike da mukamin Kwamishina a hukumar ba da tallafi ga wadanda ambaliya ya sama a jihohin da ke da gulabe da wutar lantarki a tarayyar Nijeriya, ya tattauna da manema labarai kan tsohon gwamnan Sakkwato Shehu Kangiwa a cigaban da ya samar cikin shekara biyu don zaburar da gwamnoni a yanzu su san barci ne kawai suke yi ba mulki ba.
Tsohon Gwamnan Sakkwato Alhaji Shehu Kangiwa Ya Cika Shekara 42 da rasuwa da mi ya bambanta da gwamnoni a yanzu
Tsohon Gwamnan Sakkwato Alhaji Shehu Kangiwa ya yi gwamnan tsohuwar Sakkwato wadda aka cire jihohin Kebbi da Zamfara cikinta daga shekarar 1979 zuwa 1981 shi ne zababben gwaamna na farko tun bayan samar da jihar ya yi a jam’iyar NPN cikin jamhuriya ta biyu
. Shehu Kangiwa gwamnatinsa bata yi tsawon rayuwa ba, amma an samu nasara a jagoranci, a kokarinsa na son mayar da Sakkwato ta zama gidan kowa a haujin yawon buda ido, ya samar da Otal na Giginya a birnin jiha a lokacin da aka kammala shi a shekarar 1981 kusan shi kadai ne dake da tsari a Arewa kuma ya shiga cikin manya Otal da ake bugun gaba da su a Nijeriya. Kan bunkasa bukin kamun kifi na Argungu ya zama na musamman, Kangiwa ya samar da Otal na zamani a cikin gari, har yanzu da nake Magana da kai ba a samu wata gwamnati ta gina irinsa ba domin wannan bukatar, da gwamnatinsa ta fahimci yanda harkar kasuwanci ke bunkasa a garin Gusau a can ya samar da Otal na zamani domin natsar da baki masu shigowa harkokin kasuwancin masaku da noma musamman masu zuwa daga Dam na Bakalori, da sauran abubuwan da ke bukatar kula da natuswa ya yi ba jan kafa.
Tsohon Gwamnan Sakkwato a aiyukkansa na farko bai kula da ilmi ba ne?.
Shehu Kangiwa hakan ma ya fahimci akwai bukatar tallafawa ilmi a jihar Sakkwato da gaggawa shi ne dalilinsa na samar da kwalejin Fasaha guda hudu Runjin Sambo da Durbawa da Gusau da Mafara. Ya kuma kirkiri cibiyoyin koyar da sana’a a Bunza da Ambursa da Wasagu da Tondi Yauri, abin bakin ciki da zan gayama ba wata cibiya da ke aiki a halin yanzu, an barsu sun tafi tare da wanda ya samar da su, domin ba mutane ake nufi ba. Kangiwa ya tabbatar da tsarin ba da ilmi kyauta ga duk dan asalin jihar Sakkwato tsarin har yanzu ana yinsa a jiha, ya tabbatar da makarantun Furamare da Sikandare da muke da su an samar musu kayan aiki tare da samar da kayan koyarwa ga ma’aikata a wasu makarantu. Makarantun kwana na jiha suna da komai da suke taimaka masu a wurin gasa in ta taso, a lokacinsa gwamnati ke baiwa dalibai komai kamar littafan karatu da tufafin makaranta. Kangiwa ya samar da madaba'a ta gwamnati in da anan ake buga dukkan littafai a raba su kyauta ga dalibban makaranta, daliban da suka zo daga kananan hukumomi a lokacin hutu gwamnati na ba su kudin motar komawa gida, ya kuma gina dakin karatu babba na zamani an saka littafan karatu da kowa ke bukata, bai taba yin shatar jirgin sama akai shi wata jiha da kudin al’umma, kowa ya san saukin kansa da tsantseninsa ga dukiyar jama’a domin ganin ya cika alkawalin da ya dauko wa jama’a a lokacin yekuwar neman zabensa.
Ko ba ruwan Shehu Kangiwa ne da harkar Kasuwanci da bunkasa jama’a naga ba ka ce komai kansu ba.
Ai shi gwarzo ne a bangarorin cigaban rayuwar jama'a, a bangaren cigaban harkokin kasuwanci Kangiwa ya samar da Kamfanin saka hannun jari, ya kuma gina banki hadaka na jihar Sakkwato, abin tausayi Kamfanin da banki ba wanda ke raye sun bi wanda ya kirkiro su, bayan samar da tsari mai kyau a babbar kasuwar Sakkwato, an fito da shirin tsaftar muhali in da aka samar da wurin bahaya guda 19 a birnin jiha, don tabbatar da an kacewa yin fitsari ko kashi a waje a halin yanzu ko daya babu domin wannan bukatar yanzu za ka samu mutane na fitsari a fili don ba wurin shiga da aka samar. A kokarinsa na bunkasa kananan masana'antu da samar da aiki ga matasa Kangiwa ya kirkiro Kamfanin casar shinkafa na Sakkwato da Kamfanin Sakkwato Foam da Kamfanin Tamba na abincin Kaji, da Sakkwato biredi na zamani da Sakkwato Ceramic da Sakkwato Tannery, duk a birnin jiha ya samar da su, kuma suna aiki yanda yakamata a lokacin gwamnatinsa, kamfanonin suna samar da kudin shiga da rage rashin aikin yi ga matasa a kalla kowane kamfani nada ma’aikata sun fi 50 don ciyar da jiha gaba, a yanzu ba wani kamfani daga cikinsu da ke aiki a Sakkwato sun zama tarihi. Shehu Kangiwa ya tafi da mafarkinsa na gina tsohuwar Sakkwato.
A matsayinsa na tsohon babban sakatare a gwamnatin tarayya ya roki gwamnatin tarayya a lokacin karkashin jagorancin Shugaban kasa Shehu Shagari ta yi wani abu a jiha kan haka aka yi matsaya za a yi wurin sarrafa karafa a karamar hukumar Bodinga, a yanzu in da sakatariyar Sakkwato take waton Kangiwa Sakatariya ya gina wurin ne domin saukar da bakin da za su zo daga kasar Koriya da za su yi aikin samar da Kamfanin na karafa, abin takaici bayan ya rasu aka fita batun lamarin, haka ma gwamnatin tarayya ta shirya gina asibitin kasa ta mata da yara a Sakkwato an samar da fili a tsakanin kwanar Mazuru ta Shagari da Kwanar Mazuru ta Yabo har zagaye wurin aka yi amma abin ya bi ruwa bayan tafiyarsa. Tun bayan rasuwarsa jihar Sakkwato da Kebbi da Zamfara su ke da kishirwa shugabanci nagari, a gefen samar da aiyukkan cigaba, ba ruwansu da matsa kaimi ga gwamnatin tarayya ta kawo wani aikin cigaba a jiha, in ka cire Sakkwato Rima Basin dake da hidikwata a Sakkwato ba wani aikin gwamnatin tarayya a jihohin nan, in da abin ya kara lalacewa a wadan nan jihohin an kasa yi masu hanyar mota tagwaye a kowane bangaren shigo yankin, hanyar jirgin kasa Zariya zuwa Kauran Namoda kusan za a ce ta mutu, gaba daya yankin ba a tare da shi a gefen sufuri na jirgin kasa, in dai aiki ya taso a Arewa maso yamma za ka samu ya tsaya Kaduna ko Kano, can sai a baiwa Katsina, gwamnoninmu ba ruwansu da yin korafi a kai, Shehu Kangiwa kam ba haka yake ba. Ya samu nasarorinsa ne duk a shekara biyu da yake mulki, ka auna da kanka da ya samu damar mulki tsawon shekara Takwas ya kake zaton Sakkwato za ta zama a fannin cigaba, rasuwar Kangiwa ga mutanen Sakkwato bakin ciki biyu ne, an rasa Gwamna wanda ya shirya, yake da kuma zimmar ciyar da jihar Sakkwato gaba.
Har yanzu kana ganin ba a samu madadinsa ba a Gwamnonin da ake samu a yankin Sakkwato
Har yanzu sama da shekara 40 da rasuwar sa ba a samu madadinsa ba, a shekara sama da 20 da ake mulkin dimukuradiyya tsohuwar Sakkwato da ta hada Kebbi da Zamfara sun samu gwamnoni guda 13, hudu a Sakkwato, biyar a Zamfara da hudu a Kebbi, sai dai har yanzu ba ka iya hada cigaban da suka samar da wanda Kangiwa ya samar, domin shi ya dauki aikin da gaskiya, yakan kuma ziyarci wuraren gwamnati musamman makarantun sikandare in da yake tsayawa a ci abinci tare da shi na rana da dare don tabbatar da ingancin abincin da ake baiwa yara, zai tsaya ya rika tattaunawa da dalibbai don ya san irin basirarsu da yanda ake koya masu darasi.
Ya Sakkwatawa suka ji da rasuwar Shehu Kangiwa
A ranar 17 ga watan Nuwamban 1981 Sakkwatawa suka rasa jajirtaccen dan siyasa a lokacin da yake wasan Polo a Kaduna, muna tuna shi a yanzu ne ba don ya kawo mana cigaba kawai ba, sai don zamansa na daban a cikin jagorori, ba za a mantawa da gudunmuwarsa ba a fanin kawo abubuwan da suka amfani jama'a da samar da alfanun da ake so cikin lokaci, mun yi bakin cikin da har yanzu muna tare da shi domin mun rasa jagora, Allah ya gafarta masa ya jikansa za mu cigaba da tuna shekararsa biyu ta mulki a matsayin Gwamnan Sakkwato. Margayi Sani Aliyu Dandawo a wakarsa yana cewa “Sokoto duk gwamnatin da an ka yi. An yi ta ne kawai. Ba a yi irin ta Kangiwa ba."