Gwamnatin Kaduna ta faɗi matsayarta kan rufe layukkan sadarwa a jihar

Gwamnatin Kaduna ta faɗi matsayarta kan rufe layukkan sadarwa a jihar
Gwamnatin Kaduna ta faɗi matsayarta kan rufe layukkan sadarwa a jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ba ta da wani shiri na rufe layukkan sadarwa a jihar, babu batun irin wannan mataki ko wani shiri da za a sanar.
Gwamnatin Kaduna ba ta kai kowace matsaya da hukumar gwamnatin tarayya domin ɗauke sadarwa a jihar.
Gwamnatin ta ce mutanen jihar sun fita batun jita-jitar da ake yaɗawa, labarun ƙarya ne babu tushe balle makama.

Bayanin wanda mai baiwa Hwamnan Kaduna shawara kan yaɗa labarai da sadarwa Muyiwa Adekeye ya ce mutanen jiha su fita batun labarin na ƙarya, ba za a rufe layukkan waya a jihar ba, kan harkar tsaro gwamnati bata rufa-rufa kanshi, in har za a ɗauke sadarwa a jihar za a sanar a hukumance.