Mahara sun kashe mutum 5 'yan gida daya, sun jikkata wasu a kebbi
Mahara sun kashe mutum 5 'yan gida daya, sun jikkata wasu a kebbi
Daga Yushau Garba Shanga
'Yan bindiga sunkashe mutane 5 'yan gida guda, kuma suka harbi wasu biyar a karamar hukumar Shanga Dake jihar kebbi.
Cewar wadanda suka samu rauni, 'yan bindigar sunkai masu farmaki a cikin dare yayinda suka tarar da babban yayansu Yana kiwo, suka ce malam acikin daya zaka zabi guda ko rayuwarka kokuma shanayen Dake wurinka. "yace toh zabi nagare ku duk yadda kukai Mai kyau ne.
Wakilin JARIDAR ALFIJIR HAUSA a Shanga, yayin da ya ziyarce wadannan mutanan a babban asibitin karamar Shanga Domin Karin bayanai daga bakinsu sukace.
Bayan sun harbe yayanmu, sun harbe babanmu kuma suka harbe sauran kannanmu, mukuma sukai Mana rauni, harda 'yar karamar yarinya da batasan komaiba suka harbeta da kafa, acikin wadanda suka harba mutum hudu tin alokacin suka mutu guda bamutu ba Sai lokacinda sukazo asbiti yamutu.
Agarin kauyen uchukku abin yafaru inda ainihin kabilar mutanan dukkawa ne, yanzu dai haka garin dakuma makwabtansu suna tattaki barin kauyukan izuwa sassa daban daban.
Yanzu hakan al-umman kauyukan wasu nata shigowa a garin Shanga Domin tsira da rayukkansu, sukace a tinaninsu 'yan bindigar yankin zamfara ne da sojojin najeriya ke addaba suna kokorin guduwa."
managarciya